
Daga BELLO A. BABAJI
Kimanin ƴan Nijeriya miliyan 120 zuwa 150 ne al’amarin taɓarɓarewar tsaro ya shafa a ƙasar, kamar yadda Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu ya bayyana a ranar Juma’a.
Ya faɗi haka ne a Abuja, yayin sanya hannu a yarjejeniyar MoU tsakaninsu Cibiyar Daƙile Ayyukan Ta’addanci ta Ƙasa da Cibiyar Kula da Harkokin Noma a Yankuna masu Sahara ta Ķasa-da-ƙasa.
An ƙulla yarjejeniyar ne da nufin raya kasuwancin harkokin noma da inganta rayukan al’ummar da ke rayuwa a yankunan da ke fama da matsanancin rashin tsaro.
Ribaɗu ya ce, ta’addanci abu ne da ke da mummunan tasiri ga harkar noma, wanda shi ne abinda galibin ƴan Nijeriya suka dogara da shi.
Ya kuma ce, rashin tsaro shi ne babban matsalar da ke damun kowane fanni musamman ɓangaren noma, yana mai kira da a fuskanci matsalolin da suka haddasa rashin tsaro daga tushe, waɗanda suka haɗa da talauci da rashin bada dama da nuna wariya domin magance matsalar acikin al’umma.
Ya ƙara da cewa, rikicin harkar tsaro abu ne da ke barazana ga zaman lafiyar ƙasa, waɗanda a saboda haka ne ƙasashen maƙota na yankin Sahel suka ruguje sakamakon ayyukan ta’addanci.
Haka kuma, NSA’n ya ce akwai buƙatar a yaba wa ayyukan sojoji wajen samar da hanyoyin warware matsalolin rashin tsaro da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da ci-gaba a Nijeriya.
