Wani shugaban ƙasa ya tsallake rijiya da baya bayan jirginsa ya karci ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kamfanonin Jiragen Sama da dama sun dakatar da tafiyar shiga Laberiya biyo bayan tsaikon da wani jirgin mai tashin angulu da ke ɗauke da Shugaba Joseph Nyuma ya samu, inda ya kusa kartar ƙasa a filin jiragen sama na Roberts (RIA), ranar Alhamis.

Kamfanonin Kenyan Airways, Air Peace da wasu da suka shirya sauka a Monrovia a ranar, sun dakatar da ayyuka a yayin da hukumomi ke ƙoƙarin shawo kan matsalar.

Muryoyi daga filin jirgin sun ce, jirgin ya samu tsaiko ne a lokacin da ɗaya daga cikin tayoyinsa ya fashe a yayin da ya ke ƙoƙarin sauka ƙasa, lamarin da ya jefa ƴan cikinsa cikin fargaba.

Haka kuma jirgin shi ne wanda ya ɗauko Shugaba Boakai da tawagarsa zuwa Nijeriya a farkon makon da ya gabata.

Tuni jami’an gaggawa na filin jiragen suka kai ɗauki tare da ceto shugaban ƙasar da kai shi cikin motarsa ta fadar gwamnati, inda kuma aka ɗauki ƴan tawagarsa a motar bus da ke aiki a filin jiragen.

Duk da tsaikon da aka samu, babu wanda aka rasa ko ya samu rauni, inda baki ɗayan su suka tsira.

By Babaji