Yadda gidan tarihin Waziri Junaidu ke cike da abubuwan al’ajabi

Spread the love

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Gidan tarihin Waziri Junaidu waje ne da ke tattare da kayan tarihin Daular Usmaniyya da ma magabatanta, kuma wajen da ya shafe shekaru 40 da kafuwa na cigaba da bunƙasa ta yadda ya ke samun maziyarta a ciki da wajen Nijeriya.

Gidan tarihin dai na Waziri Junaidu waje ne da aka samar domin tattara kayan tarihin mujahidan Daular Usmaniyya da sauran kayan da suka jiɓinci daular, kuma an samar da shi ne tun a shekarar 1966, watau gabanin yaƙin Basasa, wanda Wazirin Sakkwato na wancan lokaci watau Waziri Junaidu ya yi tunanin samar da waje da zai riƙa tattara wasu kayan tarihin Daular Usmaniyya da ta shafe sama da shekaru 200 da samuwa, wanda wazirin na wannan lokacin ya soma amfani da tsarin tattara kayan tarihin daga wurare daban-daban musamman gidan Sarkin Musulmi da kuma sassan Nijeriya.

A cewar babban daraktan gidan Tarihin na Waziri Junaidu, Bala Muhammad Mabera, wazirin ya cigaba da tattaro kayan tarihin daular daga wurare daban-daban yana ajiyewa a gidansa, abinda ma ya bawa masu ziyarar Sakkwato a wancan lokacin damar kai ziyara a gidan nasa kenan domin ganin kayan tarihin Daular, kuma abin da ya sanya sauƙi da sayuwa ga kayan, da sanya a shekarar 1973 gwamnatin wannan lokaci shigowa domin rungumar aikin, inji shugaban gidan tarihin.

Shugaban ya ce, karɓar ragamar aikin da gwamnatin arewacin Nijeriya ta wannan lokaci ta yi da ake kira ‘Northwestern State’ ya bata damar samar da wani waje a kusa da gidan Yarin Sakkwato na yanzu domin ajiye kayan tarihin da ta samar dama waɗanda ta karɓo daga Waziri Junaidu kuma a lokacin ana kiran wajen da Assibitin ’Yar tsaido, tare da cigaba da karɓo kayan tarihin daga sassa daban-daban na duniya.

Gidan tarihin dai na ƙunshe da kayan tarihin Daular Usmaniya, Al’adu, dama na jagororin Sakkwato na da, da kuma na yanzu dama hulɗayya tsakanin Turawan da dana yanzu.

Hakan dai tafiya ta cigaba da tafiya har zuwa shekarar 1975 da aka samar gidan tarihi sukutum aka kuma sanya masa sunan Gidan Tarihi na Waziri Junaidu domin girmamawa da gudunmawar da Waziri Junaidu ya bayar da soma tattaro kayan tarihin daular, tare da bawa gidan aikin tattara kayan tarihin daular da ke ciki da wajen ƙasar nan, dama ajiye kayan baya ga bajesu ga masu bincike da yawon buɗe ido kamar yadda dokar Jihar Sakkwato ta bawa gidan Dama.

Gidan tarihin dai na a unguwar Rogo ne, kuma yakan samu ziyarar maziyarta na ciki da wajen Nijeriya, da ɗalibai masu nazarce-nazarce, Shehunan malamai, Daktoci, dama ɗaliban sakandare da akan kawo domin nuna masu zahirin abin da malaman su kan gaya masu a azuzuwansu.

A yanzu dai gidan tarihin ya shafe fiye da shekaru 40 da kafuwa a cewar shugabansa, Bala Muhammmad Mabera kuma suna da kayan tarihin daular da suka haura sama da shekara 500 da samarwa, da kuma sassan da suka haɗa da sashen tarihi da al’adu, Littafai da rubuce-rubucen magabatan Daular, dana hulɗa tsakanin ƙasashen Turawa da magabatan daular da dai sauran su.

Tun bayan kafurwar gidan dai ya samu jagorancin magabatan da suka haɗar da Muhammadu Gwandu, Bello Mai Wurno da Ummaru Na’abu Sanyinna, Bala Abubakar, da Umaru Yabo da Abdullahi Shehu Sakkwato da Bello Idris da ya shafe fiye da shekaru ashirin yana jagorancin gidan, da Usman Ahmad Isa da kuma jagoran na yanzu Bala Muhammad Mabera.

A cewar daraktan sashen kula da kayan tarihi na gidan Junaidu, Ahmad Umar babban abinda masu ziyarar gidan suka fi mayarwa da hankali  yayin ziyarar shine kayan tarihin Shehu Usmanu musamman littafan da ya rubuta da hannunsa, ko na Abdullahin Gwandu.

By ukarofi