Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Naira, wadda ke ƙara samun karɓuwa a kan Dala duk mako, ta ƙara ƙarfi da kuzari a ranar Juma’a, inda aka sayar da ita a kan N1,580.44 a kasuwar hada-hadar kuɗi ta gwamnati.
Bayanai daga shafin intanet na Babban Bankin Nujeriya sun nuna cewa Naira ta samu N4.51 akan Dala a ranar Juma’a kaɗai.
Wannan ya nuna darajar kashi 0.28 cikin 100 daga ranar Alhamis na N1,584.95 a kasuwar hada-hadar kuɗaɗen waje na gwamnati.
Kuɗin gida ya ci gaba da kasancewa mai ƙarfi a cikin makon da ya gabata, tana samun riba a kullum.
A ranar Litinin, 19 ga Mayu, an sayar da shi a kan N1,598.68; ranar Talata, a N1,590.45; kuma a ranar Laraba, a N1,584.49.
Waɗannan nasarorin suna nuna ƙara ƙarfin gwiwar masu saka hannun jari da inganta samar da kayayyaki, yana kuma bada gudujmawa ga ayyukan naira.
A halin da ake ciki, Bankin CBN, a taronsa na kwamitin kula da harkokin kuɗi karo na 300 da ya gudana a ranakun Litinin da Talata, ya ci gaba da riƙe farashin tsarin hada-hadar kuɗi a kashi 27.5 cikin 100.
