Motoci masu lantarki za su sauƙaƙa ƙalubalen sufurin Nijeriya – Masana

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Masana Fasahar ƙere-ƙere sun ce, Motocin Maau Amfani da Lantarki (EV), fasahar idan masu ruwa da tsaki za su tallafa musu za su sauƙaƙa ƙalubalen sufurin Nijeriya da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa.

Sun bayyana haka ne a ranar Asabar a Abuja yayin da suke tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN).

Gbenga Bada, wani ƙwararre a fannin ƙera motoci a Kugbo, ya buƙaci gwamnati da ta ƙara wayar da kan jama’a game da fa’idar motocin Eɓ tare da saka hannun jari kan kayayyakin more rayuwa da za su ƙara haɓaka su.

“Yawancin ‘yan Nijeriya har yanzu ba su san fa’idar motoci masu amfani da lantarki ba.

“Har ila yau, akwai akwai buƙatar ƙarin ƙwararru don kula da EV,” inji shi.

Ya amince da ƙoƙarin gwamnati ta hanyar hukumomi kamar National Automotive Design and Deɓelopment Council (NADDC) wajen inganta tallafin Eɓ.

“Ina tsammanin sun ƙaddamar da wasu tashoshin caji na EV tare da ƙaddamar da motocin bas masu amfani da wutar lantarki a cikin gida.

“Gwamnati na da burin cimma kashi 30 a cikin harkar sufurin wutar lantarki, wanda ya dace da tsarin bunƙasa masana’antu na motoci na ƙasa.

Ya ƙara da cewa, “ƙasar Sin tana zuba jari a masana’antun EV a Nijeriya, tare da yin amfani da albarkatun lithium na ƙasar,” inji shi.

A cewarsa, ana samun ƙaruwar EV kuma alƙaluma sun nuna cewa a yanzu haka akwai tsakanin 15,000 zuwa 20,000 na motocin Eɓ a kan titunan Nijeriya a farkon shekarar 2025 wanda ya yi matuƙar ƙaruwa idan aka kwatanta da shekarun baya.

Ya kuma ce kasuwar Nijeriya tana ba da dama mai yawa don haɓakar EV tare da yawan jama’arta a birane.

Ya ce, ta hanyar shirye-shiryen kamfanoni masu zaman kansu tuni kamfanonin duniya suka fara jin kasancewarsu a Abuja da Legas.

Austin Emmanuel, masanin makamashi ya ce ta hanyar saka hannun jari a cikin EV, Gwamnatin Tarayya za ta rage hayaƙin a tituna.

Ya ce idan aka samu nasarar shigar da shi cikin harkar sufurin ƙasar zai ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar ta hanyar samar da ayyukan yi da kuma sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki.

By ukarofi