Kwastom ta samu tiriliyan N1.3 a farkon 2025 sanadiyyar sauye-sauyen Tinubu – Adeniyi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS), ta samu kuɗaɗen shiga da ya kai Naira Tiriliyan 1.3 a rubu’in farko na shekarar 2025, wanda ya ninka fiye da biliyan N600 da aka tara a daidai wannan lokacin a shekarar 2023.

Bashir Adeniyi, Kwanturolan Hukumar Kwastam ne ya bayyana hakan a wani shiri na murnar cikar Shugaba Bola Tinubu shekaru biyu a kan karagar mulki.

Ya nuna farin cikinsa kan ƙaruwar kuɗaɗen shiga, inda ya danganta hakan ga sauye-sauyen canji a ƙarƙashin Tinubu.

Adeniyi ya ce ƙaruwar kuɗaɗen shiga ya samo asali ne daga ingantattun fasahohin ayyukan tashar jiragen ruwa, ya kuma ƙara tsaurara matakan matakai a wasu hanyoyi.

“Mun tara Naira Tiriliyan 1.3 a farkon 2025 kaɗai. Hakan ya faru ne saboda yawan shigo da kaya daga ƙasashen waje.

“Kayayyakin da ake shigo da su daga ƙetare sun ragu saboda matsalolin canjin kuɗaɗen waje. Abin da ya canja shi ne inganci, gaskiya, da aiwatar da aiki,” inji Kwanturolan-Janar.

Ya bayyana cewa, hukumar na shirin ƙaddamar da shirin zamani na E-Customs, inda ya ƙara da cewa shirin na dala Biliyan 3.2 zai daidaita tsarin sarrafa kaya, sa ido, da tsarin biyan kuɗi a tashoshin jiragen ruwa da iyakokin Nijeriya.

A cewar Adeniyi, sabon shirin mai ba da izini na tattalin arziki, AEO, shirin yanzu yana shiga cikin masu shigo da kayayyaki da aka riga aka tantance, wanda ke ba da damar kasuwancin da suka dace da rage cunkoso a tashar jiragen ruwa.

By ukarofi