
Daga BELLO A. BABAJI
Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya Fina-finai ta Ƙasa (MOPPAN) tare da haɗin-gwiwar reshenta na Jihar Kebbi, ta Karrama Gwamnan jihar, Dakta Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) kan bai wa mawaƙa da wasu ƴan harkar masana’antar fina-finai guda 100 muƙaman masu taimaka masa, wato SA’s.
Kakakinta, Ibrahim Amarawa a wata sanarwa ya ce lambar yabon da aka bai wa gwamnan wani ɓangare ne na ƙoƙarin shugabancin MOPPAN wanda zai ƙara ɗaukaka martabar ƙungiyar a idon shugabanni da al’umma.
Haka kuma ya ce, taron karramawar ya yi nasarar samun halartar jagororin MOPPAN daga jihar.
Sannan, hakan ya nuna cewa ƙungiyar ta samu damar cigaba da hulďa da gwamnatoci domin bunƙasa masana’antar fina-finai a Nijeriya musamman Kannywood.
