Ma’aikatan gwamnatin Katsina fiye da 6000 suka sami horo kan sarrafa kwanfuta

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A ƙokarin gwamnatin Dikko Raɗɗa na sake fasalin aikin gwamnati, ma’aikatan jihar fiye da 6000 suka kammala samun horo kan sarrafa kwanfuta.

Mai ba gwamna shawara kan sake fasalin ayyukan gwamnatin jihar Alhaji Usman Isyaku ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a ofishin sa.

Ya ce gwamnati za ta cigaba da bada irin wannan horo har ga ɗaukacin ma’aikatan jihar,manufa a nan gwamnati na sa ran maida harkokin aiki zuwa manhajar zamani,kuma dole sai duk ma’aikaci ya koyi sarrafa kwanfuta.

Alhaji Usman ya bayyana wasu daga cikin sabbin tsare tsaren tafiyar da aikin gwamnati da suka haɗa da gudanar da jarabawa a rubuce kafin ma’aikaci ya kai ga muƙamin babban sakatare.

Haka kuma duk wani ma’aikaci da ya cancanci ƙarin girma sai ya zauna jarabawa a rubuce,inji mashawarcin gwamnan.

Mashawarcin gwamnan ya bayyana cewa wannan gwamnati, a shirin ta na sake fasalin ayyukan gwamnati ta ƙirƙiro da hukumomi tare da haɗe wasu da kuma soke wasu gaba ɗaya.

Ciki kuwa akwai hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da yanzu haka tana nan tana sauraren wasu ƙorafe-ƙorafe a wasu bankuna da ya shafi hannun jari da ƙorafi kan rabon takin zamani.

A kan ƙaranci ma’aikata kuwa Alhaji Usman Isyaku yace gwamnati ta fara tantance ma’aikata a ma’aikatu da hukumomin gwamnati domin ta gano adadin ma’aikatan da kowace hukuma ke buƙata.

Haka suma ma’aikatan da zaune suke a ofis basa aikin komai,za a tura su wararen da ake buƙatar ma’aikata a cewar sa.

By ukarofi