Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
A ci gaba da ƙoƙarin tallafawa mabuƙata, uwargidan gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta bayar da tallafin kayan Sallah ranar Juma’a ga dubban mata marasa galihu a faɗin jihar.
Hajiya Larai Musa Lawal da Hajiya Hussana Sani Muhammad sune suka wakilci Uwargidan gwamnan, Hajiya Huriyya a wajen rabon kayayyakin, inda ta bayyana cewa an bayar da tallafin ne domin rage wa mata nauyi a lokutan bukukuwa da kuma ba su damar gudanar da bukukuwan Sallah cikin farin ciki.
Kayayyakin sun haɗa da shanu, raguna, kayan abinci, da tsabar kuɗi ga waɗanda suka ci gajiyar tallafin da aka zaɓo daga dukkan ƙananan hukumomi 14 da ke jihar.
Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta buƙaci al’ummar Zamfara da su yi amfani da lokutan Sallah wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya da neman taimakon Allah wajen magance matsalolin tsaro da jihar da ƙasa baki ɗaya ke fuskanta.
Ta kuma jaddada cewa jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal za ta ci gaba da ƙarfafa wa mata gwiwa a wani ɓangare na ci gaban rayuwar su.
Rabon tallafin ya shafi mata ‘yan siyasa na jam’iyyar PDP, kansiloli, shugabannin matan ƙananan hukumomi, dattawan mata, da waɗanda suka ci gajiyar gidauniyar Hajiya Huriyya Dauda Lawal Trust Fund da dai sauransu.
A nata jawabin, wata ‘yar siyasa Hajiya Hadiza Mai H ta yabawa uwargidan gwamnan bisa wannan karimcin, inda ta bayyana tallafin a matsayin wanda ya dace.
