
Daga BELLO A. BABAJI
Biyo bayan sauya sheƙa da Gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Umo Eno ya yi a ranar Juma’a, kansiloli a ƙananan hukumomin jihar sun juya masa baya da cewa ba za su bi shi zuwa APC ba domin bai shawarce su ba kafin ya ɗauki matakin a matsayinsu na zaɓaɓɓun ƴan siyasa.
Wani kansila da yan emi a sakaye sunansa ya ce hakan wulaƙanci ne a gare su, saboda haka lallai sai ya neme su tare da tattaunawa da su kafin a warware matsalar.
Ya kuma ce, tuni wasu daga cikinsu suka yanke shawarar sake tsayawa takara a PDP a karo na biyu.
Haka kuma, ya ce gwamnan sai da ya tattauna da ƴan majalisu a jiha da matakin ƙasa da ciyamomi, amma su ya mayar da su saniyar ware, lamarin suka bayyana a matsayin wulaķanta su da gwamnan ya yi.
Hallau, ya bayyana cewa waɗanda ya shawarta ba masu cin zaɓe ne a yankunansu ba ba tare da kansiloli ba.
