Jihohin da za a iya samun ambaliya a Nijeriya cikin watan Yuni – NiMet

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta ce akwai yiwuwar a fuskanci ambaliyar ruwa a wasu jihohin Nijeriya, musamman na arewa ta tsakiyar ƙasar.

NiMet ta bayyana haka ne a cikin hasashen yanayi da ta yi na wannan wata na Yunin 2025, wanda ya kama a ranar Lahadin da ta gabata.

Rahoton na zuwa ne yayin da ƙasar ke ci gaba da jimamin wata mummunar ambaliyar ruwa da aka samu a jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar ƙasar, wadda ake kyautata zaton ta yi sanadin rayuka sama da 500.

NiMet ta ce duk da cewa yanzu ne damina ke kankama a yankin arewacin ƙasar, amma “ana hasashen samun marka-markan ruwan sama a cikin ƙanƙanin lokaci a wasu jihohin arewacin ƙasar, musamman Nasarawa, Filato, Bauchi, Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi da kuma yankin Babban birnin tarayya (Abuja).

“Wannan zai iya haifar da ambaliyar ruwa a wuraren da suke cikin haɗari,” inji rahoton na NiMet.

Daga nan sai rahoton ya buƙaci mutane su kasance a ankare tare da bibiyar bayanan da take fitarwa a kai a kai.

Haka nan NiMet ta buƙaci hukumomin da ke kula da madatsun ruwa su sanya ido sosai tare da lura da cikowar ruwa a madatsun.

Rahoton ya ce jihohin kudancin ƙasar da kuma na arewa ta tsakiyar ƙasar za su samu ruwan sama mai ƙarfi da iska a kai a kai.

Duk da haka NiMet ɗin ta ce jihohin Kwara, Kogi, Niger, Nasarawa, Benue, Taraba, Adamawa, Kaduna, Kano, Katsina, Sokoto, Edo, Delta da kuma Abuja ba za su samu ruwan sama mai yawa kamar yadda suka saba samu ba.

Wanda hakan ya sanya hukumar ta bai wa manoma shawarar su yi amfani da ilimi da kuma ƙwarewa wajen harkokin noma.

By ukarofi