Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya karrama ɗaya daga cikin hamshaƙan attajiran duniya, Bill Gates da lambar yabo ta CFR.
An yi bikin karrama attajirin ne ranar Talata a birnin Legas.
Attajirin shi ne mai fitaccen kamfanin fasahar nan na Microsoft da kuma gidauniyar Bill Gates.
A watan da ya gabata ne dai attajirin ya alƙawarta rabar da kashi 99 cikin 100 na dukiyarsa da aka ƙimanta za ta kai dala biliyan 200 ga marasa galihu nan da 2045.
Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ne ya sanar da haka a wani saƙo da ya wallafa a shafin na Tiwita mai suna @aonanuga1956.
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Legas a ranar Talata da daddare ya ba da lambar girmamawa ta ƙasa ga hamshaƙin attajirin nan Bill Gates, wanda ya kafa Microsoft kuma wanda ya kafa gidauniyar Bill Gates,” inji Onanuga a cikin saƙon.
An yi imanin cewa, an ba da wannan karramawar ne saboda la’akari da irin gudunmawar da Gates ya bayar ga harkokin kiwon lafiya da ci gaban duniya, musamman a Nijeriya, ta hanyar tallafawa da daɗewar gidauniyar ta sa kan harkokin kiwon lafiyar jama’a, da alluran rigakafi, da kuma yunƙurin kawar da fatara.
Gates ya ci gaba da ƙulla alaƙa mai ƙarfi da Nijeriya kusan shekaru ashirin, inda gidauniyarsa ta zuba jari a shirye-shiryen da suka shafi kawar da cutar shan inna, bunƙasa noma, da ƙarfafa tsarin kiwon lafiya.
CFR, ɗaya daga cikin mafi girman karramawa na ƙasa, ana bayar da shi ne a al’ada ga ɗaiɗaikun mutanen da suka ba da gudunmawa sosai ga ci gaban ƙasar.
