Dalilina na neman Tinubu ya kori wasu ministoci da shugabannin tsaro – Kalu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Sanata Orji Kalu, mai wakiltar Abia ta Arewa, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya sauke wasu ministoci da shugabannin tsaro daga aiki, saboda rashin sanin makamar aiki da kuma rashin tasirin su ga ci gaban Nijeriya.

Da yake jawabi yayin shirin Siyasa a Yau, wani wani shiri da gidan Talabijin na Channels ta gabatar a ranar Litinin, Kalu ya ce ya tantance majalisar ministocin tarayya mai ci a yanzu.

“Wasu mutanen da ke aiki tare da Shugaba Tinubu ya kamata a sauke su daga aiki, dole wasu su tafi – daga ɓangaren tsaro da kuma cikin ministoci,” inji shi.

Kalu, wanda tsohon gwamnan jihar Abia ne, ya kuma shawarci shugaban ƙasar da ya yanke shawara mai tsauri domin daidaita gwamnatin sa da abin da ’yan Nijeriya ke buƙata.

“Dole ne shugaba Tinubu ya jajirce wajen korar wasu daga cikin waɗannan ministocin. Idan ya ɗauki shawarata – yawancin waɗannan ministocin, na tantance su kuma na yi magana da shi a asirce – ya kamata yawancin su su tafi, wannangaskiya ce,” inji shi.

Ya aara da cewa, akwai buƙatar a maye gurbin wasu shugabannin tsaro idan har ana so Nijeriya ta shawo kan ƙalubalen da take fuskanta.

“Idan ya ɗauki shawarata, wasu daga cikin shugabannin tsaro ma za su tafi, babu wani son zuciya game da gwara Nijeriya idan har da gaske muna son mu gwara ta,” inji shi.

Bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, Shugaba Tinubu ya naɗa ministoci 45 – majalisar ministoci mafi girma tun bayan komawar Nijeriya turbar dimokuraɗiyya a 1999.

Waɗannan naɗe-maɗe sun haifar da damuwa da yawa da kuma ra’ayoyi daban-daban a lokacin.

A watan Oktoban 2024, shugaban ƙasar ya aiwatar da wani babban sauyi a majalisar ministocinsa. An kori ministoci biyar, ya naɗa sabbin ministoci bakwai, sannan wasu goma aka sake naɗa su a sabbin mukamai.

Canje-canjen ya shafi manyan ma’aikatun da suka haɗa da ilimi, yawon shaƙatawa, harkokin mata, ci gaban matasa, da gidaje.

Musamman ma, Ma’aikatar Raya Neja-Delta ta koma Ma’aikatar Raya Yankuna, an narkar da ma’aikatar wasanni, an haɗe ma’aikatun yawon buɗe ido da fasaha da al’adu.

Tun bayan da shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur a shekarar 2023, ‘yan Nijeriya sun fuskanci tashin farashin man fetur, tsadar rayuwa, da sauye-sauyen tattalin arziki waɗanda suka kawo wahalhalu cikin ƙanƙanin lokaci.

Da yake magana kan halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki, Kalu ya amince da ƙoƙarin da shugaban ƙasar ya yi na sake fasalin aasar amma ya ce har yanzu tasirin bai kai ga mafi yawan ‘yan Nijeriya ba.

By ukarofi