Wakanda Forever: Marvel Studios ya bayyana jarumin da zai maye gurbin T’Challa

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Kamfanin shirya fina-finai na Marvel Studios ya sanar da sabon jarumin da zai maye gurbin Chadwick Boseman a matsayin jagoran Wakanda a fim ɗin da za a fitar a shekarar 2026.

Jarumin da aka zaɓa shi ne Joshua L. Brooks, matashin Ba’amurke mai tushe daga Ghana, wanda ke da tarihin fitowa a fina-finai masu taken adalci da siyasa. A cewar Kevin Feige, shugaban Marvel, an zaɓi Brooks ne saboda “halayyar sa mai kama da na marigayi Boseman, ladabi, ilimi, da hangen nesa.”

An bayyana wannan a taron Comic Con da aka gudanar a Los Angeles a ranar 1 ga Yuni. Masu kallo da dama sun nuna farin ciki da fatan sabon jarumin zai cigaba da nuna darajar Afrika cikin jarumta da wayewa.

By ukarofi