Ya kamata a dawo da tallafin aikin hajji ga maniyyatan Nijeriya – Ndume

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban kwamitin majalisar dattijan Nijeriya kan harkokin ƙasashen waje a lokacin aikin hajjin 2025, Sanata Ali Ndume ya buƙaci da a mayar da tsarin bayar da tallafi kan batun aikin hajji a ƙasar domin rage tsadar kujera ga maniyyata.

Ndume ya faɗi haka ne a tattaunawarsa da BBC jim kaɗan bayan kammala aikin hajjin 2025 a ƙasar Saudiyya.

Sanatan wanda ya nuna gamsuwa kan tsarin da aka samar ga mahajjatan Nijeriya a Saudiyya ya ce “dama gwamnatin da ta shuɗe ita ce ta cire tallafin da ake bayarwa kan aikin hajji, saboda haka ya kamata a dawo da bayar da tallafi saboda aikin hajjin ya yi tsada.”

Mahajjatan Nijeriya a 2025 sun biya kuɗin kujera ne tsakanin naira miliyan 8.3 zuwa miliyan 8.8 dangane da ɓangaren ƙasar da suke zama.

Hakan ya ɗara abin da maniyyatan Nijeriya suka biya kan kujerar aikin hajji a bara – 2024, inda suka biya fiye da naira miliyan shida a kan kujera.

Sai dai batun aikin hajji a Nijeriya a shekarar 2024 ya kasance mai cike da ruɗani sanadiyyar zargin badaƙala da rashin kyakkyawan tsari, lamarin da ya kai ga bincike da kuma sauke shugaban hukumar.

Farashin kujerar aikin hajji ya ci gaba da tashi a Nijeriya shekara bayan shekara, lamarin da yawanci akan ɗora alhakin kan durƙushewar darajar takardar kuɗin ƙasar ta Naira.

By ukarofi