June 12: Shettima ya jinjina wa MKO Abiola bisa gudumawarsa ga dimokraɗiyya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya ce tarihin fafutukar tabbatar da dimokraɗiyya na daya daga cikin tunawa da marigayi Cif Moshood Kashimawo Olawale Abiola, wanda ya yi daidai da ranar 12 ga watan Yuni.

Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, a yayin taron bikin murnar cikar dimokraɗiyya a Njeriya shekaru 26 da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja.

Ya kuma bayyana marigayi Abiola a matsayin ɗan kishin ƙasa wanda ya miƙa wuya domin ƴan Nijeriya.

Ya ƙara da cewa, sadaukarwar Abiola ta zama abin koyi ga dimokraɗiyya kasa.

Shettima ya ci gaba da cewa, Nijeriya ba za ta manta kishi da jajircewar da mazan fama da su kayi ba a fafutukar yunƙurin kafa dimokraɗiyya a ƙasar nan.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma ce, ko shakka babu shugaba Tinubu ya ɗauki alƙawarin hidimta wa dimokraɗiyya da dukkan ɗan Najeriya gami da gina ƙasar.

Marigayi MKO Abiola “abin tunawa ne mutum ne mai kishin cigaba da son tsarin mulkin dimokraɗiyya.

Har’ilayau, Shettima ya buƙaci ƴan Nijeriya da su tashi tsaye don gina dunƙulewar dimokraɗiyya a Nijeriya, yana mai bayyana ta a matsayin “Gidan da ba za a iya mantawa da shi ba, wanda babu wani abu da zai iya rushe tubalin gidan.”

“Kowanenmu a nan yana da muhimmin aiki na goyon bayan yunƙurin shugaban ƙasa don samar da tsarin mulki dimokraɗiyya da gina al’umma.”

By Babaji