
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin cigaba da bada kariya ga ƴancin tofa albarkaci baki da dimukraɗiyya ta bai wa ƴan Nijeriya dama akai.
A lokacin da ya ke jawabin Ranar Dimukraɗiyya a zauren Majalisar Dokoki a Abuja, ranar Alhamis, Tinubu ya faɗa wa wakilan jami’an tsaro cewa kada su riƙa matsa wa masu sukar gwamnatinsa, waɗanda suke ganin tsare-tsarensa ba su yi musu ba ko kuma suna ɗauke da matsi.
Ya ce, a tsarin dimokraɗiyya sai an samu juriya game da suka da zage-zage don haka ko da al’umma za su riƙa kiransa da wasu sunaye mara daɗi, hakan ba zai sa ya gajiya ba wajen tabbatar da ƴancinsu kamar yadda tsarin mulkin ƙasar ya bada dama.
Haka kuma, Tinubu ya yi kira ga masu goyon bayansa a siyasa da ƴan majalisu da su riƙa fifita tattaunawa akan tsangwama da ƙaurace wa ƙoƙarin nuna danniya wa al’umma.
Ƴan jarida da ɗaiɗaikun al’umma da dama sun sha fuskantar barazana game da suka da suke yi wa gwamnatin Tinubu da zargin su da taka dokar haramta aikata laifi ta yanar gizo ta 2015 da wasu dokokin ƙasa daga hukumomin tsaro.
Saidai duk da haka, Shugaba Tinubu a yayin jawabin nasa ya jaddada cigaba da tabbatar da ƴancin tofa albarkaci baki, waɗanda ba su ci karo da dokokin ƙasa ba acikin al’umma.
