Na yi kuskuren sukar Jonathan, inji Bello El-Rufa’i

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ɗan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i kuma ɗan majalisar wakilai a yanzu, Bello El-Rufa’i ya yi da-na-sanin sukar gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Johnathan.

Bello, wanda ke wakiltar mazaɓar Kaduna ta Arewa ya ce a rashin sani ne ya sa bai san cewa akwai shugabanci ba a zamanin gwamnatin Goodluck.

Ya ce, ya gano hakan ne a lokacin da ya ga mahaifinsa ya ziyarci tsohon shugaban ƙasar domin tattauna bututuwan da suka shafi siyasa.

Lamarin da ya sa ya fahimci cewa, haƙiƙancewa da ya ke yi a baya wajen sukar gwamnatin Goodluck kuskure ne duba da yadda El-Rufa’i ya ce zai je wajensa da nufin ya ba shi shawara akan harkar shugabanci.

Haka kuma ya bayyana goyon bayansa ga gyare-gyaren da aka samu a harkokin zaɓe ciki har da aika sakamakon zaɓe ta kwamfuta.

By Babaji