
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar Sojojin Isra’ila ta ce ta ƙaddamar da hari akan sojojin Iran da ma’ajiyar makaman nukiliyarta dake Babban Birnin ƙasar, Tehran.
Akan haka ne Shugaban Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya gargaɗi Isra’ila da cewa ta tsammaci mummunar sakamako ga abinda ta aikata, wanda ya yi sanadin hallaka da yawa daga cikin kwamandojin sojojinta da manyan masana kimiyya.
A wani saƙo ta bidiyo da Fraministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya fitar da safiyar Juma’a, ya ce harin an zartar da shi ne da nufin nakasa albarkatun makaman nukiliyar Iran.
Shugaban jami’an sojojin Isra’ila, Eyal Zamir ya ce ƙarfin makaman nukiliyar Iran ya kai matakin da Isra’ila ba za ta iya cigaba da zura masa ido ba ba tare da ta yin wani yunƙuri ba domin cigaba da kare wanzuwarta.
A sanarwar da Shugaban Iran ya fitar akan harin, ya bayyana cewa lallai ba za su lamunta ba, don haka Isra’ila ta shirya wa yaƙi.
