
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Juma’a ne Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta sanar da kama wani ɗan ƙasar Chana a yayin wani atisayen daƙile ayyukan ta’addanci da jami’an sojoji suka gudanar a Jihar Borno.
Duk da cewa ba a bayyana sunansa ba, sojoji sun ce mutumin ya ce yana aikin haƙar ma’adanai ne, wanda a yanzu yana riƙe a hannunsu.
Hakan ya faru ne ƙasa da mako ɗaya da kama wasu ƴan Pakistan guda huɗu a shiyyar Arewa maso Gabas, waɗanda ke bada horo ga ƴan ta’adda.
Wata majiya daga sojoji ta shaida wa manema labarai cewa, ana zargin ɗan Chanan da jagorantar samar wa mayaƙan Boko Haram kayan aiki da cinikayyar makamai.
Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Markus Kangye a wata takarda, ya ce an kama mutane biyar da laifin samar wa Boko Haram kayan yaƙi.
Ya kuma ce, an kama su ne a Ƙananan Hukumomin Kukawa da Ngala a Borno da kuma Geidam a Jihar Yobe a tsakanin ranakun 5 da 7 na watan Yuni, 2025.
Kazalika, ya bayyana cewa ɗan Chanan na ɗaya daga cikin mutanen biyar waɗanda suke taimaka wa mayaƙan, inda a yayin haka ne aka ƙwato mota, babur, wayoyin salula, fasfo na Chana da Naira 10,000.
