Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Nijeriya ta ce akwai yiwuwar za a samu raguwar mace-macen mata masu juna biyu a yayin haihuwa da kashi 20 cikin ɗari kafin nan da shekarar 2027.
ƙaramin Minstan Lafiyar Nijeriya Iziaƙ Salako ne ya bayyana hakan, inda ya ce gwamnatin ƙasar na kuma ƙokarin cimma muradin ganin an samu raguwar mutuwar jarirai da yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar da kimanin kashi 15 cikin ɗari.
Gwamnatin ta bayyana matakai daban-daban da za su taimaka wajen cimma hakan kamar samar da kayan aiki, da horo ga Jam’ian lafiya.
Wata ƙwararriya a fannin kula da lafiyar mata ta ce hakan abu ne mai yiwuwa ganin irin matakan da gwamnati ta ɗauka a baya bayannan kamar kula da lafiya kyauta, da samar da motocin ɗaukar marasa lafiya cikin gaggawa, da kuma gano yankunan da ke da yawan mace-macen mata domin lalubo musabbabin hakan don magance shi.
Rahotanni na bayyana cewa gwamnatin Nijeriya dai na ware kashi 5 cikin 100 ne kawai a fannin lafiya wanda bai kai kashi 15 da aka nemi kowacce ƙasa a Afirka ta ware ba.
Nijeriya dai ƙasa ce da aka fi samun mace-macen mata masu juna biyu a duniya, kamar yadda wani bincike da BBC ta gudanar ya tabbatar.
