Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi fatali da buƙatun Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, sannan ta ci shi tarar Naira 100,000.
Kotun, wacce ke ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Hamman Barka dai ta yi watsi da buƙatun ne kan ƙarar da aka shigar ranar 21 ga watan Mayun 2025, bayan neman buƙatar janye ƙarar da aka ɗaukaka.
Buƙatun dai na ƙunshe ne a cikin wasu ƙararraki masu lamba Cɓ/395/M1/2025 da kuma Cɓ/395/M2/2025, waɗanda aka shigar a ranakun uku da kuma 25 ga watan Mayun 2025, wanda a cikinsu aka ambaci sunan Akpabio a matsayin mai ɗaukaka ƙara.
Waɗanda ake ƙara kuma su ne Sanata Natasha da Magatakardar Majalisar Dokoki ta ƙasa da Majalisar Dattawa da shugaban kwmaitin ɗa’a, ladabtarwa da ƙorafe-ƙorafen jama’a na majalisar, Sanata Neda Imasuem.
Tun farko dai a cikin ƙarar, Akpabio ya nemi kotun da ta ƙara masa lokacin da zai iya ƙalubalantar hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke mai lamba FHC/ABJ/CS/384/2025, wanda ta yanke ranar 10 ga watan Maris 2025 bisa hujjar cewa akwai kura-kurai a cikinsa.
Sai dai da take yanke nata hukuncin, kotun ta ce ta amince da buƙatar janye ƙararrakin guda biyu, kamar yadda mai ƙara ya buƙata.
Sai dai ta ce ta ci mai ƙarar tara Naira 100,000, waɗanda za a ba wacce aka yi ƙara.
