Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Zazzaɓin Lassa da ke haddasa mutuwar ɗimbin ‘yan Nijeriya a duk shekara, nan ba da jimawa ba za a yi rigakafinta, inji wani masani.
Wani fitaccen masanin cutar huhu kuma babban jami’in kamfanin Innoɓatiɓe Biotech, Simeon Agwale, ya faɗa a ranar Asabar cewa rigakafin zazzaɓin Lassa da wani ɗan Nijeriya ya samar yana inganta ta hanyar gwaji a kan ɓeraye da na dabbobin daji.
Agwale ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a Abuja.
Ya ce wannan ci gaban da aka samu ya sanya fatan shawo kan cutar mai saurin kisa.
‘Yan Nijeriya da dama ne ke mutuwa duk shekara sakamakon zazzaɓin Lassa.
Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta ba da rahoton cewa sama da mutane 138 ne suka mutu daga cutar tsakanin watan Janairu zuwa 15 ga Mayu tare da adadin masu cutar da kashi 19.3 cikin 100.
Rahoton ya bayyana cewa adadin ya haura daga kashi 18.0 cikin 100 da aka rubuta a cikin lokaci guda a shekarar 2024.
Rahoton ya kuma ce an samu adadin mutane 717 da aka tabbatar sun kamu da cutar a mako na 18, inda sabbin jihohi huɗu (Ondo, Edo, Bauchi da Benuwai) suka bayar da rahoton ɓullar cutar a cikin makon nan kaɗai.
Rahoton ya bayyana cewa kashi 71 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun fito ne daga jihohi uku: Ondo, kashi 30 cikin 100, Bauchi, kashi 25 cikin 100 da Taraba, kashi 16 cikin 100, wanda ke nuni da cewa ana ci gaba da fama da matsalar duk da matakan da ake ɗauka a facin aasar.
Agwale ya ce rigakafin, wanda kamfanin Pac-Man Biologics ya ba da lasisi daga Jami’ar Melbourne, ya nuna kariya 100 cikin 100 yayin gwaji.
“Wannan maganin da wani ɗan Nijeriya ya yi shi ne kaɗai ya zuwa yanzu ke nuna inganci a kan nau’in kwayar cutar Lassa ta Nijeriya, wadda ta sha bamban da nau’in Josiah da aka fi amfani da shi daga ƙasar Senegal.
“Muna da keɓantaccen lasisin rigakafin don amfani a Afirka. Muna biyan kuɗin ga Jami’ar Melbourne kuma ta haka ne tsarin ƙirar ke aiki.
“Wannan shi ne kariyar kashi 100. Yana nuna babban alƙawari, kuma muna fatan kammala gwajin na farko nan da nan,” inji shi.
