Zan iya mutuwa a kan APC, inji Uzor Kalu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon Gwamnan Jihar Abia, Orji Uzor Kalu, ya sake jaddada cewa a shirye ya ke ya ba da ransa akan jam’iyyar APC, musamman a jihar Abia.

Ya bayyana haka ne a hirarsa da manema labarai a garinsu na Igbere, Jihar Abia.

Da aka tambaye shi ko APC na da wata dama ta kayar da jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2027 a jihar Abia, Kalu wanda ke wakiltar Abia ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya ce shi da sauran magoya bayan APC za su yi aiki tuƙuru domin nasarar shugaban ƙasa a jihar.

Ya ce; “APC na da ƙarfi a Abia. Kamar yadda na faɗa a wata hira, a shirye nake in ba da raina saboda jam’iyyar. Ni mamba ne na APC kuma mai tsayawa kan gaskiyar jam’iyyar. Ni cikakken ɗan APC ne. Shi ya sa APC ke da ƙarfi a Abia ta Arewa.

“Jam’iyyarmu za ta yi aiki tuƙuru domin ganin shugaban ƙasa ya yi nasara a jihar. Mun taɓa yin hakan a baya, kuma za mu sake yin hakan a shekarar 2027.”

By ukarofi