Rashin adalci da son kai a PDP ya sa muka bar ta – Mustapha Inuwa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Babban jam’iyyar adawa ta PDP a Katsina na gab da rugujewa, hakan ya biyo bayan ficewa da jiga jigan ya’yan jam’iyar keyi.

Na baya bayan nan sune ƙungiyar tsaffin yan takara na jam’iyar adawa ta PDP a jihar da suka sauya sheka zuwa sabuwar tafiyar a Jihar Katsina.

Tsaffin yan takarar da suka sauya sheka su 287 sun haɗa da yan takarar kujerar ɗan majalisa 24 da na kujerar shugabancin ƙaramar hukuma su 13 da su kayi takara a shekarar 2022 da 2025.

Sai ‘yan takarar kujerar kansila 240 da suka fito daga ƙananan hukumomi 34 da ke jihar.

Da yake jawabi shugaban sabuwar tafiyar Mustapha Inuwa ya bayyana rashin adalci, gaskiya da son zuciya yasa su da wasu jiga jigan ya’yan jam’iyar ta PDP suke kafa sabuwar tafiyar da ta ƙunshi haɗakar jam’iyun a kasar.

Ya ce a nan Jihar Katsina rashin gaskiya da ke cikin hidimar sayasar ya sa suka koma gefe guda suka kafa sabuwar tafiya da za ta daƙile wannan rashin adalci.

“Zamu tabbatar da wannan sabuwar tafiya zamu bar al’amuran na wannan tafiya ga jama’a kuma a shirye muke muyi tafiya da kowa.

Mustapha Inuwa wanda ya taɓa riƙe tsagin shugabancin jam’iyar PDP a Jihar kafin kafa wannan sabuwar tafiya ya tabbatar wa tsaffin ‘yan takarar cewa yanzu sun zama ‘yan kwamitin da ake zama ana tattauna duk wani abu da ya shafi wannan sabuwar tafiya.

Sanata Ahmed Babba Kaita wanda jigo ne a sabuwar tafiyar ya bayyana jin daɗin sa kan yadda sabuwar tafiyar ta sami karɓuwa da mutane ke tururuwa zuwa shiga sabuwar tafiyar da ba a daɗe da kafa ta ba.

Ya tabbatar wa mutanen da suka shigo sabuwar tafiyar cewa za su yi iyakar bakin yinsu wajen kawo babban sauyi a Jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya.

Ya kuma sanar da cewa nan da mako guda zasu tsaida matsaya wajan fidda jam’iya a ƙasar domin kawar da mulkin zalunci a ƙasar baki ɗaya.

Shugabannin ƙungiyar tsaffin ƴan takarar suma sunyi jawabi inda suka jaddada goyon baya da biyayyar su ga sabuwar tafiya tare da alƙawarin bada ta su gudunmawar da duk ya kamata ga tafiyar.

By ukarofi