Daga AISHA ASAS
A cikin ‘yan watannin da suka gabata, duniya ta kasance cikin firgici yayin da rikici tsakanin Isra’ila da Iran ya ƙara ƙamari. Hare-haren iska, musayar wuta ta ƙarƙashin ƙasa, da kuma kalaman yaki daga ɓangarorin biyu sun ƙara jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin wani yanayi na barazana ga zaman lafiya. Wannan sabuwar fuskantar rikici tsakanin manyan abokan gaba a siyasar yankin na da matuƙar tasiri a kan al’ummar Falasɗinu, waɗanda suka shafe shekaru fiye da saba’in suna fafutukar neman ‘yanci daga mamayar Isra’ila.
Iran da Isra’ila sun shafe shekaru suna adawa da juna. Iran na kallon Isra’ila a matsayin barazana ga musulmi, musamman ma al’ummar Falasɗinu, yayin da Isra’ila ke zargin Iran da ɗaukar nauyin ƙungiyoyin da ke kai mata hari, kamar Hamas da Hezbollah. A shekarar 2024 zuwa 2025, abubuwa suka ɗauki sabon salo bayan Iran ta kai farmaki kai tsaye kan Isra’ila, wani lamari da ba a saba gani ba a baya, wanda hakan ya janyo martani mai zafi daga Isra’ila da mayar da martani ta hanyar kai hari cibiyoyin soja na Iran a Syria da Lebanon.
Ba yau aka fara jin irin zafin da ke tsakanin Isra’ila da Iran ba. Tun shekarar 1979 bayan juyin juya hali a Iran, ƙasar ta daina amincewa da Isra’ila, tana kallonta a matsayin ‘gaɓar’ da ke hana yankin samun zaman lafiya. A ɓangare guda kuma, Isra’ila na kallon Iran a matsayin babban haɗari ga tsaronta da tsaron abokan aikinta.
A ƙarshen watan Afrilu 2025, duniya ta tsinkayi wani abin da bai taɓa faruwa ba a tarihi: Iran ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami kai tsaye akan Isra’ila, wani mataki da ya girgiza duniya gaba ɗaya. Isra’ila kuwa ta maida martani da ruwan bom a cibiyoyin soji na Iran a Syria da Iraƙ. Daga wannan rana, aka shiga wani sabon fage na rikici, mai kyau? Ko mai muni?
Yayin da hanjin duniya ke kaɗawa da ƙarar makamai, kuma sararin sama ta birkice da gubar rokoki, al’ummar Falasdinu na ci gaba da zama cikin inuwa mai duhu. Rikicin da ke tsananta tsakanin Iran da Isra’ila ya koma wani sabon salo na faɗa ta kai tsaye, wato ba mai wakilci ko wata kafar tsaka ba, abin da ke ƙara tsananta barazana ga dukka yankin Gabas ta Tsakiya.
Yayin da mutanen da ke goyon bayan Falasɗinawa ke murna da wannan rikici, duba da cewa, Iran ta kasance tsaran juna wadda ta fi dacewa ta gwabza da Isra’ila, domin ko za ta ɗibi na dafuwa a jikin Iran, to tabbas Iran ɗin za ta ɗibi na gashi a jikinta, sakamakon ƙarfin makaman yaƙi da ta ke da shi wanda ya saɓa wa na Falasɗin. Saidai babu wanda ya zauna ya yi tunanin tasiri ko abinda zai iya kai ya kawo ga ƙasar da ita Isra’ila ta jigata, wato Falasɗin, wadda ta kasance tsakiyar wannan faɗa.
A cikin wannan fadan na manyan giwaye, Falasɗinu na kasancewa cikin yashi mai kaifi. A Gaza, West Bank, da yankunan da ke ƙarƙashin mamaya, rayuwar ɗan adam ta zama daraja marar tsada. Babu ruwan su da rikicin kai tsaye, amma duk lokacin da Isra’ila ke yaki da Iran ko Hezbollah, to Falasdinawa na fuskantar wata baraza ta harin sama, rufewar hanyoyin agaji, da kisan kiyashi. Duk da cewa a wani ɓangare hakan ya kawo sauƙi a kisan kiyashin da ita Isra’ila ke yi a Gaza, sakamakon mayar da hankali da ta yi kan babbar barazana gare ta, wato Iran wadda ta kasance tsara da ita. Domin bincike ya nuna, akwai yiwar idan Isra’ila ba ta samu tallafi daga ƙawayenta irin su Amurka ba, to fa da yiwar Iran ta kai ta ƙasa.
Idan mun yi waiwaye kan ra’ayoyin mutane kan lamarin, wasu na ganin jinjina da al’ummar musulmai ke yi wa Iran a matsayin mai kishin Musulunci sam bai cancance ta ba, domin a cewar su, faɗan da Iran ke yi da Isra’ila ba tana yi ne ba don Falasdinawa, tana yi ne don daɗaɗar hamayyar da ke tsakaninta da ƙasar ta Isra’ila.
A cewar Dr. Fawaz Gerges daga London School of Economics:
“Falasɗinu ta zama tambarin siyasa da ake zubar da jini a kansa. Iran na amfani da batunta don ɗagawa, Isra’ila na amfani da ita don kariya, amma babu mai kare ‘yan ƙasa na gaskiya.”
Wannan furuci na Dakta Fawaz ya sha suka damartani da dama, domin da yawa na ganin, ko da kuwa ba da gaske Iran ke kishin Musulunci ba, hakan sasauci ne ga Falasdinu, domin za su taimaka wurin raunana Isra’ila da kuma saka ‘yan ƙasar tursasawa gwamnatin su neman sulhu sakamakon kisan da ake masu, wanda hakan zai iya kai wa ga sharaɗin tsagaita wuta a Gaza ko kai ƙarshen yaƙin Falasɗin da ita Isra’ila. Wanda hakan ba ƙaramin cigaba ba ne ga rayuwar bayin Allah da ke cikin ƙunci a yankin ba. Wannan kuwa abin so ne ga duk wanda ke iƙirarin zuciyarsa na ƙuna kan abinda ake yi wa al’ummar Falasɗinu.
A gefe guda, rikicin Isra’ila da Iran na rage ƙarfin Isra’ila wajen mayar da hankali gaba ɗaya kan Gaza da West Bank. Wannan na iya zama wata dama ga ƙungiyoyin Falasɗinu su samu karin ƙarfin fada.
Wasu kwararru da ‘yan kishin Falasɗinu na fatan wannan rikici zai ja hankalin duniya, har ƙasashen Yamma su matsa wa Isra’ila lamba don sulhu. Ana kallon cewa, lokacin da Isra’ila ta shiga yaƙi da ƙasa mai ƙarfi kamar Iran, ba za ta iya mai da hankali sosai akan Gaza ba, wanda zai iya ba Falasdinu damar sarari da kariya.
A daya ɓangaren kuwa, akwai haɗarin cewa, Falasdinu za su ci gaba da zama kamar filin gwajin makamai tsakanin Isra’ila da abokan gaba kamar Iran. Har ila yau, idan har rikicin ya rikiɗe zuwa yaƙi na gaba da gaba tsakanin ƙasashen, zai iya janyo ƙarin hasarar rayuka da halaka gine-gine a Gaza da Lebanon, inda Iran ke da tasiri ta hannun Hezbollah.
Wani rahoto daga Al-ƙuds Al-Arabi ya nuna cewa:
“Duk wani yaƙi tsakanin manyan da ke iƙirarin kare Falasdinu, yawanci yana ƙarewa ne da ƙarin mutuwar Falasɗinawa.”
Wasu ƙasashen Larabawa sun ɗauki matakin shiru ko diflomasiyyar gefe. Kamar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, suna ƙoƙarin daidaita tsakaninsu da Isra’ila domin moriyar tattalin arziki. Wannan ya rage ƙarfin goyon bayan Falasɗinu daga Larabawa. ƙasashen yamma kuwa, sun fi mayar da hankali kan hana yaɗuwar yaki tsakanin Iran da Isra’ila fiye da kare ‘yancin Falasɗinu.
Masu ruwa da tsaki a rikicin Gabas ta Tsakiya na bukatar sake nazarin tasirin farmaki da mayar da martani. Falasdinu na buƙatar taimako na haƙiƙa, na diflomasiyya, agaji, da matsin lamba a matakin ƙasa da ƙasa, ba kawai makamai da hayaniya ba.
Ya kamata ƙasashen musulmai da masu ruwa da tsaki su zamo garkuwa ta haƙiƙa, su samar da dandalin sulhu da taimakon kwarai maimakon barazana da yaki.
Ko da yake rikicin Isra’ila da Iran yana da haɗari sosai ga zaman lafiya a duniya, yana kuma nuna yadda rikicin Falasdinu ya mamaye zukatan musulmi da ƙasashen Gabas ta Tsakiya. Amma har yanzu ba a samu wata tabbatacciyar shaida cewa wannan rikici zai kawo ‘yanci ga Falasdinu. Har sai an samu haɗin gwiwar kasa da kasa da shirye-shiryen diflomasiyya masu inganci, al’ummar Falasɗinu za su ci gaba da fuskantar ƙalubale.
Saidai tambayar da ke yawo kan ƙwaƙwalwar mutane Musulmai, shin kawar da kai da ƙasashen musulmai ke yi daga halin da ƙasar Falasɗinu ke ciki koyarwar Musulunci ce?
An sanar da mu a hadisi ingantacce cewa, “Musulmi ɗan uwan musulmi ne.” Kenan duk abinda ya shafe shi ya shafe ka. Don haka wajibi ne musulmi ya ba wa musulmi kariya idan har yana da ikon yin hakan.
Saidai yadda zai yi hakan ne ke buƙatar nazari. Idan mun duba, Musulunci addinin zaman lafiya ne, da haka wasu ke ganin matakin da Saudiyya ta ɗauka shi ne daidai, wato ta kai agaji da kuma kira da a zauna lafiya. Saidai abin tambaya me ta yi na janye alaƙa da ƙasar da ke cin zarafin ‘yan uwanta musulmai? Shin ta yanke alaƙa da ita? Ta sanya takunkumi gare ta? Ta yi barazanar ba wa Falasɗinu kariya idan ba a zauna teburin sulhu na haƙiƙa ba?
Idan mun koma ɓangaren Iran, ta yi yadda ƙasashen Turai ƙawayen Isra’ila suka yi, wato fitowa fili ta bayyana goyon baya ga ƙasar ta Falasɗinu, ta yi kira ga sauran ƙasashe abokanin tarayya a addini da su yi yadda ta yi. Ta ɗaga murya sosai don haka kowa ya shaida da ƙoƙarin ta ga al’ummar Falasɗinu. Saidai ba za mu kawar da kai kan cewa, ba don Falasdinawa take faɗa da Isra’ila ba, ba kuna don ba su kariya ba.
Saidai mun san hakan zai iya taimakawa ƙasar ta Falasɗinu. Amma abin tambaya anan shi ne, ko ta yi tunanin yadda za ta ba wa Falasɗinawa kariya yayin da take kai farmaki a Isra’ila?
Idan akwai lokacin da ya kamata a ajiye bambancin aƙida a Musulunci, to fa wannan ne lokacin da ya kamata mu rataye shi, har Musulunci ya fita daga barazanar mamaya da Isra’ila ke da ƙudurin yi ga ƙasashen musulmai.
Aya a cikin littafi mai tsarki ta ce, “Wannan ce hanya ta madaidaiciya, kada ku bi ‘yan hanyoyi, sai ta rarraba kawunanku…….”
Yayin da musulmi ke ganin duk wanda bai bi inda ya bi ba, ko wanda ba irin kalarshi ba, ko wanda ba mutumin garinshi ba, to fa ba cikakken musulmi ne a idonsa ba, to tabbas a lokacin ne za a ci Musulunci da yaƙi.
Domin idan har musulmai na duniya za su haɗe kai, su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, da tabbas ba wata ƙasar da ta isa ta ɗaga masu yatsa. Domin duk wani abu da ake buƙata a duniya na ƙarfin iko akwai shi a ƙasashen musulmai. Tun daga albarkatun ƙasa, arziki zuwa hikimar ƙera nakamai. Abinda kawai suka rasa shi ne kishin addininsu.
