Burina shi ne idan na mutu a riƙa tunawa da ni a matsayin mai ƙaunar Nijeriya – Gowon

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, ya ce yana fatan a riƙa tunawa da shi a matsayin shugaba mai ƙaunar Nijeriya da mutanenta idan ya mutu.

Gowon ya shugabanci Nijeriya daga 1966 zuwa 1975.

A wata hira da gidan talabijin na Arise, dattijon mai shekaru 90 ya bayyana wasu sabani da ba a iya sasanta su ba, waɗanda suka haifar da barkewar Yaƙin Basasar Nijeriya a watan Yulin 1967.

Gowon ya ce yana fatan a riƙa tunawa da shi a matsayin ɗan Nijeriya mai ƙaunar ƙasarsa da kuma mai yi mata addu’a.

Ya ce: “Ina so a riƙa tunawa da ni a matsayin wanda ke ƙaunar ƙasarsa Nijeriya, wanda ke ƙaunar ’yan Nijeriya, wanda ke addu’a aƙalla idan ba zan iya yaƙi ba, ina addu’a domin Nijeriya ta ci gaba da kasancewa ƙasa da dukkanmu muke so. Na san babu wata ƙasa da za ta iya zama cikakkiyar ƙasa ba tare da matsala ba.”

By ukarofi