Gwamnatin Tarayya ta sammaci kamfanin Air Peace kan ƙorafe-ƙorafen fasinjoji

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin Hukumar Kare Haƙƙin Gasar a Tsakanin Kamfanoni ta Tarayya, ta gayyaci mahukuntan Kamfanin Air Peace, biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da fasinjoji suka yi dangane da rashin mayar da kuɗin tikitin jirgi duk da cewa kamfanin ya soke tashin jirage.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar mai ɗauke da kwanan watan Yuni 3, 2025, ta umarci Air Peace da ya bayyana a hedikwatarta da ke Abuja a ranar Litinin, 23 ga watan Yuni, 2025, domin magance ƙorafe-ƙorafen jama’a da kuma zargin take haƙƙin masu amfani da jirgin.

Wata sanarwa da daraktan hulɗa da kamfanoni, Ondaje Ijagwu, ya fitar ta bayyana wannan umarni a ranar Litinin a Abuja.

Ijagwu ya bayyana cewa ayyukan kamfanin jirgin sun saɓa wa sashe na 130 (1) (a) da (b) da kuma 130(2) (b) na dokar kariyar gasa ta tarayya ta 2018, wanda ke ba kamfanoni damar gaggawar mayar da kuɗaɗe idan har ba su isar da ayyuka ga jama’a ba.

Ya bayyana cewa an bayar da sammacin ne bisa ga sashe na 32 da na 33 na dokar, inda ya buƙaci Air Peace ya bayar da wasu hujjoji na musamman.

Wannan ya haɗa da kundin koke-koke na batutuwan da suka shafi ƙin mayar da kuɗaɗe cikin watanni 12 da suka gabata, bayanan duk kuɗaɗen da aka samu zuwa yau.

By ukarofi