Daga USMAN KAROFI
Wasu ‘yan bindiga sun kashe tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙaramar hukumar Tarka a Jihar Benuwai, Aondoakaa Yaiyol. Marigayin wanda aka kashe a daren Juma’a, yana riƙe da muƙamin kwamandan hukumar masu tsaro na dazuka wato Nigeria Hunters and Forest Security Services a lokacin da lamarin ya faru.
Rahotanni sun bayyana cewa Yaiyol ya rasa matarsa a shekarar da ta gabata cikin yanayi makamancin haka, inda aka kashe ta tare da ƙone gidansa. Kakakin yaɗa labarai na PDP a jihar, Tim Nyior, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai ranar Asabar.
Mai ba gwamna Hyacinth Alia shawara kan harkokin tsaro, Chief Joseph Har, ya bayyana kisan a matsayin “sake kai hari ga kwamanda”, inda ya ce ‘yan bindigar sun zo da babur, suka harbe shi daga sannan suka tsere. Bincike na farko ya nuna cewa wani daga cikin waɗanda suka kashe matarsa wanda aka ɗaure a gidan yari, ya fito, kuma suna ta rikici tsakaninsu har zuwa wannan lokaci.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, DSP Udeme Edet, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’ansu sun fara farautar waɗanda ake zargi. Ya ƙara da cewa ‘yan sanda sun bi sawun wanda ake zargi zuwa mafakarsa amma ya tsere kafin isowarsu. Edet ya tabbatar da cewa za a kama wanda ya aikata kisan nan bada jimawa ba.
