Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Masarautar Gaya da ke Jihar Kano ta sanar da sauke Alhaji Usman Alhaji, tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, daga sarautar Wazirin Gaya.
A wata wasiƙa da aka aika masa, masarautar ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne sakamakon wasu “yanayi da ba za a iya kauce wa ba,” kuma sauke shi ya fara aiki nan take.
Ta cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na yankin Gaya Munzali Muhammad Hausawa ya sanya wa hannun ya bayyana cewa Sakataren Masarautar Gaya, Alhaji Bello Halilu, ya yabawa gudunmuwar da Alhaji Usman Alhaji ya bayar a lokacin da yake riƙe da sarautar. Ya gode masa bisa goyon bayan da ya bai wa masarautar da kuma ƙoƙarinsa wajen raya al’adun gargajiya na masarautar.
Masarautar ta ce wannan mataki na nuna jajircewarta wajen kiyaye mutunci, kima da darajar sarautar kamar yadda al’ada ta tanada.
Ba a bayyana cikakken dalilin tuɓe rawanin tsohon sakataren gwamnatin Kanon ba.
“Wannan mataki yana tabbatar da ƙudirin masarautar na kare mutunci da darajar sarautun gargajiya kamar yadda al’ada ta tanada,” a cewar sanarwar
Wannan lamari ya faru ne mako guda bayan Alhaji Usman Alhaji, kuma shugaban ƙungiyar APC Patriotic Volunteers na ƙasa, ya soki Gwamna Abba Kabir Yusuf a wani taron manema labarai a Kano.
Ya zargi gwamnan da kasa cika alƙawurran yaƙin neman zaɓe duk da kuɗaɗen da jihar ke samu daga FAAC da sauran hanyoyi.
Alhaji, wanda ya taɓa zama sakataren gwamnatin Jihar Kano a mulkin Ganduje, ya ce mutanen Kano, ba tare da la’akari da jam’iyya ba sun cancanci shugabanci nagari kuma suna da ‘yancin dimukraɗiyya na neman hakan.
