Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Maiduguri
Wani ɗan ƙunar baƙin-wake ya tayar da bom da misalin ƙarfe 10:00 na daren ranar Jumma’a da daddare a gaban wani gidan wasanni dake kusa da kasuwar kifi, a garin Konduga ta Jihar Borno.
Sakamakon fashewar bom ɗin, kimanin mutane 11 ne suka rasa rayukan su, sa’ilin da ƙarin wasu adadi mai yawa suka samu mabambantan raunuka, ta dalilin ƙunar baƙin-waken.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ƴan sanda a Jihar Borno, ASP Nahum Daso, da safiyar ranar Asabar, ya bayyana cewa sama da mutane 10 ne suka mutu a harin bom ɗin, ya ƙara da cewa suna gudanar da bincike don gano adadin waɗanda suka jikkata.
“Jiya Jummu’a, da misalin ƙarfe 22:00 na dare, a garin Konduga, wani mutum ya kutsa kai cikin taron jama’a inda ya tayar da bam din dake jikinsa, hakan ya jawo mutuwar sama da mutane 10.” In ji shi.
Ya ce rundunar su ta tura tawagar jami’an tsaro, Sojoji da ƴan-sanda zuwa garin, domin dawo da al’ammura bisa doka da oda, saboda a samu cikakken tsaro.
“Ana ci gaba da gudanar da bincike don gano abin da ya faru. Saboda har yanzu muna tattara bayanai dangane da harin ƙunar baƙin-waken.” Ya nanata.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, babu wata ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai wannan harin, amma a lokuta da dama an sha zargin ƙungiyar Boko Haram da kai irin waɗannan hare-hare a Arewa Maso Gabashin Nijeriya da ma wasu sassa.
Haka zalika kuma, wannan harin ƙunar bakin-waken ya zo ne bayan da sojoji suka daƙile wani harin da ‘yan ta’adda suka kusa kaiwa a ƙaramar hukumar Gwoza da Kukawa a jihar.
