Kano: Bom ɗin sojoji ya halaka mutane biyar da raunata wasu da dama

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mutane biyar sun rasu a yayin da wani abin fashewa da aka yi zargin na jami’an sojoji ne ya tarwatse a Kano.

Haka kuma wasu guda 15 sun samu munanan raunuka.

Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin ya auku ne a safiyar ranar Asabar, inda tuni jami’an tsaro da na bada agajin gaggawa suka garzaya wajen da abin ya faru.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, wanda ya ziyarci wajen jim-kaďan da faruwar al’amarin, ya ce ta yiwu bom ɗin a ƙarƙashin ikon sojoji ya ke wanda aka gaza kula da shi yadda ya dace.

Ya bayyana cewa, an gaggauta kai waɗanda lamarin ya shafa asibitoci mafi kusa.

Kwamishinan ya kuma ce, suna bincike akansa, inda a yanzu sun gano cewa motar da abin ya rutsa da ita an taho da ita ne daga Jihar Yobe.

Kawo yanzu hukumomi ba su tabbatar da asalin musabbabin faruwar al’amarin ko mamallakansa ba, wanda da zarar an kammala bincike, za a bayyana wa al’umma cikakken bayani a kai.

By Babaji