Rundunar sojin sama sun halaka ‘yan bindiga da dama a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rundunar sojojin sama ƙarƙashin ‘OPERATION FANSAN YAMMA’ sun hallaka ƴan bindiga da dama a yankin ƙaramar hukumar Ƙanƙara.

Farmakin da sojojin suka kai ya biyo bayan bayyanan sirri kan maɓoyan yan ta’addan a ƙauyukan Sanusi Dutsinma da Sanusi Iku kusa da Dutsen Matallawa da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara.

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya fitar da sanarwar haka ga manema labarai a Katsina.

Haka kuma ya ƙara da cewa rundunar sojojin sun kashe ƴan bindigan da dama a bayan wata makarantar sakandare da ke garin Ƙanƙara bayan da ƴan bindigan suka kai wa motan yaƙi na yan sanda hari, “Sojojin sun kashe ƴan bindigan da dama wasu suka gudu ɗauke da mayan raunuka,”inji Dr Ɗanmusa.

Harwala yau rundunar ‘OPERATION FANSAN YAMMA’ sun hallaka wasu ƴan bindigan a maɓoyan su da ke wasu yankunan Ƙanƙara a lokacin da suke ƙoƙarin kaucewa da ɗaruruwan Shanu da suka sata.

Dr Nasiru Ɗanmusa ya jaddada ƙudirin gwamnatin jihar Katsina tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na kawo zaman lafiya da tsaro a jihar.

Kwamishinan yayi kira ga al’ummar jihar da su taimakawa jami’an tsaro ta hanyar basu bayanan sirri kan maɓoyan yan ta’adda da sauran ɓata gari a fadin jihar.

Ya ce hare haren rundunar sojojin sama zai cigaba har sai an kakkaɓe yan ta’adda a jihohin Arewa maso Yammacin ƙasar da maido da zaman lafiya a yankin.

By ukarofi