DSS ta gayyaci Sheikh Masussuka a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gayyaci fitaccen malamin addinin Musulunci xan asalin Jihar Katsina, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, a cikin makon da ya gabata.

Sheikh Masussuka ya tabbatar da amsar gayyar ta hukumar DSS sai dai ya ce hukumar ta gayyace shi ne, don tattaunawa da shi game da yadda za a samar da zaman lafiya a qasa.

“Na samu gayyata daga DSS inda aka ce ana buqatar gani na a ranar 19 ga watan Yuni, 2025. Jin haka sai na sanar da lauyoyina. Mun je ofishin na DSS, don mu ji me ke faruwa. Daga qarshe mun tattauna da DSS game da samar da zaman lafiya a qasa, saboda duk abin da ake so a cimma ba zai yiwu ba sai ana zaman lafiya,” inji Sheikh Masussuka.

Sai dai wasu na ganin hukumar ta gayyace shi ne, saboda irin fatawowin da yake yaxawa da ake zargin sun ci karo da koyarwar addinin Musulunci da aka saba da su, waɗanda ke haifar da cece-kuce a qasar nan musamman arewacin Najeriya.

A yayin da malamin yake zantawa da manema labarai a Katsina, bayan hukumar ta DSS ta sallame shi, Sheikh Masussuka ya bayyana cewa, ya san akwai mutanen da suke adawa da irin da’awar da yake yi a qasar nan a halin yanzu, saboda haka ne ya zarge su game da gayyatar da DSS ɗin ta yi masa, sai dai ya buqaci xalibai da magoya bayansa akan kada su takali mutanen da wata rigima.

“Mu mun san waxanda suke adawa da wannan da’awa. Ba mu nufin kowa da sharri, muna nufin kowa da alhairi, kuma ko da sun zage ni kada ku neme su da rigima,” inji shi.

Sheikh Masussuka ya jaddada matsayarsa ta aiki da Alƙur’ani zalla, inda malamin ya ce bai yarda da wasu manyan littattafan addinin Musulunci ba irinsu Bukhari da Muslim.

“Ni dai na tabbatar abin da na ce ban yarda da shi ba a addini shine Bukhari da Muslim kuma waɗannan littafan ban san sadda qasar nan ta wajabta su cewa kowa sai ya yarda da su ba, sannan cikin littattafan da Allah ya aiko babu Bukhari da Muslim, amma na san ya aiko Annabi Muhammadu (S. A. W) da kuma Alƙur’ani. Saboda haka na yarda da Alƙur’ani kuma na yadda da kundin tsarin mulkin qasa, amma ban yarda da Bukhari da Muslim ba,” inji malamin.

Sheikh Masussuka ya yi suna musamman a kafafen sada zumunta na zamani wajen bayar da wasu fatawowi da wasu ke ganin ka iya haddasa rigama, musamman ga mutanen da ba su yi imani da fahimtarsa ba.

Har zuwa haɗa wannan rahoton hukumar DSS ta Katsina ba ta yi ƙarin haske ba game da musabbabin gayyatar Sheikh Masussuka ba.

By ukarofi