Barcelona ta ɗauki golan Espanyol Joan Garcia

Spread the love

Barcelona ta ɗauki mai tsaron raga Joan Garcia daga Espanyol bayan ta biya kuɗin da ke cikin yarjejeniyarsa da kulob ɗin na yuro miliyan 25.

Matashin mai shekara 24 zai koma Barca ranar Juma’a a hukumance, inda zai saka hannu kan kwantaragin shekara shida.

An sha alaƙanta Garcia da ƙungiyoyin Arsenal da Manchester United amma sai ya zaɓi ya ci gaba da zama a ƙasarsa Sifaniya.

Ya buga wa Espanyol wasa 67 tun bayan shiga tawagarta a 2021. Sai dai bai fara buga wa Sifaniya wasa ba tukunna.

Barca na son ta sama wa golanta Marc-Andre ter Stegen magaji, wanda ya shafe akasarin kakar da aka kammala a benci bayan ya ji rauni a watan Satumba.

By ukarofi