Filippo Inzaghi ya karɓi aikin horar da Palermo

Spread the love

Kungiyar Palermo mai buga ƙaramar gasar firimiya ta Italiya ta naɗa tsohon tauraron wasa Filippo Inzaghi a matsayin kocinta.

Inzaghi – wanda yayan tsohon kocin Inter Milan ne Simone Inzaghi – ya bar ƙungiyar Pisa bisa fahimtar juna duk da samun damar buga Serie A a bana da suka yi ƙarƙashin jagorancinsa.

A jiya Talata ne Palermo ta sanar da naɗa tsohon ɗan wasan gaban na Italiya kan kwantaragin “shekaru da dama”.

Inzaghi mai shekara 51 ya shafe akasarin shekarun ƙwallonsa a Juvntus da AC Milan, inda ya ci kofin Serie A biyu da Champions League biyu a Milan ɗin, kuma yana cikin tawagar Italiya da ta ci Kofin Duniya a 2006.

Yanzu babban aikin da ke gabansa shi ne dawo da Palermo babbar gasar Serie A bayan faɗuwa daga gasar tun 2017.

By ukarofi