Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray a wannan Alhamis ɗin ta sanar da ɗaukar ɗan wasan Jamus, Leroy Sane daga Bayern Munich.
ƙungiyar ta Turkiyya ta ɗauki ɗan wasan ne kyauta bayan kwantaraginsa ya ƙare a Munich.
Sane mai shekaru 29 ya rattaba hannu kan kwantaragin shekaru uku inda zai riƙa ɗaukar albashin Yuro miliyan 9, kwantankwacin Dala miliyan 10.4, duk shekara kamar yadda kulob ɗin bayyana.
Sane ya buga wa ƙasarsa ta Jamus wasanni 70, inda kuma ya lashe kofunan Bundesliga guda huɗu a Bayern Munich tun bayan raba gari da Manchester City, inda ya dauki Firimiyar Ingila guda biyu.
A kakar bana Sane ya jefa ƙwallaye 13 a duk gasannin da ya haska, inda ya taimaka wa Bayern lashe gasar Bundesliga bayan ta suɓuce daga hannunta a kakar bara.
