NAHCON ta kwaso maniyyata 14,000 daga Saudiya

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar Hajji ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da cewa ta kwaso fiye da maniyyata 14,000 daga ƙasar Saudiyya zuwa Najeriya. Wannan ya biyo bayan kammala aikin hajjin bana na shekarar 2025, wanda ya samu nasarar tafiya lafiya.

Rahoton da NAHCON ta fitar daga cibiyar Command and Control dake birnin Makkah ya bayyana cewa, maniyyatan daga Jihar Sakkwato da babban birnin tarayya Abuja ne aka fara kwasowa. Jirgin Flynas mai lamba XY9082 ya bar Jeddah zuwa Sakkwato da ƙarfe 7:51 na safe, ɗauke da maniyyata 422 da jami’ai 4.

Bayan haka, wani jirgi mai lamba XY9022 ya sake tashi daga Jeddah zuwa Abuja da ƙarfe 10:33 na safe, inda ya ɗauko maniyyata 425 tare da jami’ai 4. Wannan ya kai adadin maniyyatan da aka dawo dasu zuwa 14,014 a cikin jirage 33 da aka kammala tashi da su zuwa gida Najeriya.

NAHCON ta tabbatar da cewa tana cigaba da sa ido tare da haɗin gwiwa da hukumomin jiragen sama da na tsaro domin tabbatar da sauka lafiya da tsari na dukkanin maniyyatan Najeriya. Hukumar ta bayyana ƙudurinta na ganin an kammala kwaso dukkanin maniyyata cikin nasara da kulawa.

By ukarofi