Gwamnatin Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutane 30 a harin Zuru

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnatin Jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutum 30 a wani sabon hari da ‘yan bindiga suka kai a yankin Zuru. Shugabannin ƙananan hukumomin Zuru da Danko Wasagu, Muhammad Gajere da Hussaini Bena, sun bayyana cewa mutane 16 ne suka mutu a garin Tadurga, yayin da 14 suka rasa rayukansu a garuruwan Kyebu da Yar Kuka da ke cikin yankin Waje.

Sun bayyana hakan ne lokacin da mataimakin gwamnan jihar, Sanata Umar Tafida, ya kai ziyara zuwa Tadurga ranar Juma’a. Sun ce harin ya jikkata mutane da dama, tare da sace dabbobi da wasu kayayyaki masu daraja daga hannun mazauna yankin.

Sanata Tafida, wanda ya wakilci Gwamna Nasir Idris, ya miƙa sakon ta’aziyyar gwamnati ga al’umman Tadurga da Kyebu, yana mai cewa gwamnati na ɗaukar matakan gaggawa don tabbatar da tsaro da kuma hana ‘yan bindiga samun damar sake kai hari. Haka kuma, ya roki Allah ya gafarta wa mamatan da ya bai wa iyalansu haƙurin jure rashi.

Hakimin Dabai, Alhaji Suleman Dabai, ya yaba da yadda gwamnatin jihar ta gaggauta ɗaukar mataki, yana mai danganta sauyin tsaro da nagartar shugabancin Gwamna Idris. A cikin irin goyon bayan da gwamnatin ta nuna, Sanata Tafida ya bayyana bayar da tallafin naira miliyan 50 ga al’umman da abin ya shafa – miliyan 25 ga Tadurga da miliyan 25 ga Kyebu domin rage musu raɗaɗin wannan masifa.

By ukarofi