Gada-gadar Trump za ta shafi mutuncin Amurka a yau!

Spread the love

Da ganin yadda a yau abubuwa suka nunawa duniya shine yadda shugaban mutanen Amurka, wato shugaban gada-gada Mista Donalt Trump yake yin abinsa kamar ɗan rano! Gaskiya kowa ya fara cewa Amurka ƙasa ce babba, amma ta shiga tasku saboda shugabannin da suke zaɓa yawancinsu kamar iblis ya shige su, domin ɗaukar kansa duniya. Ga ababen da suka faru lokacin shugaban Reagan na kaiwa Libya hari har suka so su kashe shi, ya nuna cewa wasu daga cikin shugabannin Amurka sun kusa da ace dasu wata Kalmar turanci “paranoid” wato masu taɓin hankali kusan ababen da sukeyi na ganin sun ɗauki cewa sai wanda suka ga dama zai yi mulki cikin duniya kususan, na latin amurka zuwa ƙasashen larabawa zuwa Afrika, wacce itace ma “tiɓis-tiɓis” domin ganin yawancin juyin mulkin ana zargin daga manyan ƙasashen turai da Amurka su suke ɗaure gindin ayi, matuƙar shugaba yaso yace dasu kowa ya riƙe inda yake, wato babu tsoma baki kenan! 

Kaga Faransa da Ingila sune suka kasance shugabannin mulkin mallaka a duniya kususan a afrika, su ake zargi ta ciki ofisoshinsu na “diflomasiyya” ana zargin yawancinsu ma’aikata ne masu leƙen asirin ƙasa ne. ta cikinsu sukan samo abokan burminsu inda wai suke shirya kawar da dukkan waɗanda suke kuskurewa ra’ayinsu ko yi musu gardamar ta yaya zasu tafiyar da ma’adanan ƙasashensu, kususan man fetur da iska gas, tagulla, zinare, gwal da sauransu. ɗauki yadda sukayi da wani shugaban Iran wanda yace dole ne Iran ta ringa juya rijiyoyin manta, ba wata ƙasar waje ba kamar yau, ukun nan wato Amurka, Ingila da Faransa, su ukun suna cikin manyan shugabanni masu faɗa aji a majalisar ɗinkin duniya. To shi wancan shugaba na Iran bashi kaɗai bane, domin sun yiwa Libya da wata ƙasa a Latin Amurka ta wani wai shi “Orega” kai hatta Saddam Hussain Allah Ya ji ƙansa sanadin sun juya shi yaƙi juyuwa, shine ya sa suka shirya masa gadar zare ba kamar yadda wasu suke ra’ayin yahudanci suke fassara Sharif Saddam kamar kwikwiyon amurka ko Ingila bane!

Gaskiyar Biden shugaban da trump ya gada yayi rugu-rugu da dukiyar amurka, na ziga shugaban zilenski na Ukren ya shiga yaƙi da Rasha wacce yau shekaru huɗu kenan kamar yadda Marigayi Alhaji Garba sufa yake cewa “abu kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba! Yau Amurka ta shiga ruɗanin tattalin arziƙi ba’a gane haka ba sai lokacin da shi donalt trump ya hau mulki! Shi Trump ya sami kansa cikin ruɗu, ganin dama Amurka tana taƙama da ƙarfin tattalin arziƙin ƙasa, sai gashi sun shiga “recession” kuma duniya ta soma ganin haka shine shi shugaba Trump ya fito da wasu tsauraran matakai na firgita ƙasashen duniya kamar China da ƙawayensa na Turai kamar Ingila, Faransa da Kanada, wacce tace da shi suma fa mutane ne, kuma ƙasa mai ‘yancin kanta, duk a inda ya yi musu domin durƙushesu zasu fito fili su rama. 

Haka ita kanta uwar gulma, wato Ingila ita ma tace “inda ɗillin takanyi ɗillin fa” kaga yadda Donalt Trump ya ɗauki ƙoƙo yaje wajen Saudiyya, ƙatar da Daular Larabawa wanda ya samo kuɗaɗe masu yawa wasu sunce tiriliyon biyu na Dala wasu sunce malala gashin tinkiya! To kaga dai yadda larabawa suka zama yaran cikin gidajen yahudu da nasara waɗanda suke ko suka kashe larabawa tsantsan a gazza ƙasar larabawa wanda a yanzu suke cikin uƙuba kuma duniya ta yi shiru, kamar zabi ake kashewa, kuma amurka itace take ɗaurewa yahudawa gindi, irinsu Netanyahu suke yin kisan kiyashi ga waɗannan ƙabilar larabawa. 

Ka ga dai sarkin saudiya baice komai ba a gaban Trump game da kisan gillar da ake yiwa waɗannan bayin Allah; abin kaico idan ka duba hoton sosai shi sarkin riƙo na Saudiyya ya yi tsi-tsi kamar yaron Trump. Allah Ya kiyaye naka ya lalace. Yanzu dai su sarakuna da masu riƙe da mulki a duniya sun ɗauki cewa duniya ta turawa ce da kurum waɗanda suke so wato yahudu kenan ko? To jama’ar duniya ahuwonku ance idan tururuwa ta fara fuka-fukai to sauran sai su fara shirin yaƙi.

Daga Comrade ibrahim abdu zango.

Chairman: Kano unity forum,

Kano – Nigeria, 08175472298

By ukarofi