ZUWA GA IYAYE: Mu hana ’ya’yanmu cin zali

Spread the love

Matsalar cin zali wata matsala ce da iyaye da dama suka ƙi mayar da hankalinsu a kai, wata matsala ce da iyaye ba su damu da ita ba tunda ‘ya’yansu ke zaluncin ba su ake zalunta ba.

Ga yara da dama da ke fuskantar cin zali a makaranta, tabon da cin zalin ke bari a rayuwarsu abu ne mai zurfi kusan a ce fiye da ciwon da ke kan fatarsa.

Asusun Kula da ƙananan Yara na Majalisar ɗinkin Duniya, UNICEF, ta ce damuwar da al’ummar duniya ke nunawa tana ta’azzara a kan buƙatar tsare lafiyar kwakwalwar ɗaliban makaranta.

Akwai nau’ikan cin zalin da dama kamar;

Cin zali na jiki: Wanna ya haɗa da duka da jefa dutse ko wani abu daban da tofawa wani yaro yawun baki da laƙaba wa wani yaro sata da ƙwacewa sauran yara kayansu da sauransu.

Yayin da cin zali na jiki ke haifar da lahani ga jikin yaro, wannan nau’in cin zalin na haifar da lahani na ƙwaƙwalwa.

Irin wannan mugun nufi da wulaaanci daga wasu yaran na lalata tunanin yaran da aka zalunta na kansu da na matsayinsu a makaranta har da ma matsayinsu a duniya.

Zage-zage: Wannan ya haɗa da zagi mai cutarwa da tsokana da kiran wasu yaran da sunayen da bai dace ba saboda wani yanayi na halittarsu da wulaƙanci, da tsoratarwa, da kalaman nuna wariya har da na launin fata da cin zarafi da aibantawa, da cin zalin yaran da ke yawan shiru ko ba su cika magana ba da dai sauransu.

Cin zalin da jama’a suke yi: Wannan ya haɗa da harara domin tsoratarwa da cire wasu daga cikin wasu ƙungiyoyi, da tsegumi ko yaɗa jita-jita, da sanya wasu su zama kamar wawaye, da lalata mutuncin mutum da dai sauransu.

Cin zali a shafukan sada zumunta: A nan kuwa, za a ga yadda ake yaɗa abubuwan tsana idan wani ya ɗora hotonsa ko ya wallafa wani saƙo, da har zai saka mutum ya ji kamar duk an fi shi a duniya, wasu ma har suna kashe kansu kan irin waɗannan abubuwan.

Cin zali na launin fata: Wannan ya haɗa da wulaƙanta mutane saboda ƙabilarsu ko kalar fatarsu ko al’adarsu da sauransu.

Cin zali kan addini: Wannan kuma ya haɗa da zaluntar mutane saboda asalin addininsu ko aƙidarsu.

Cin zali kan masu nakasa: Wannan shi ne ƙin yi hulɗa da wani ko gudun wani ko yi musu mugun nufi saboda suna da nakasa da sanya wani ya ji ba daɗi, ko yin barkwanci don cutar da wani saboda rashin lafiya ko nakasa.

Cin zali na jinsi: Wannan ya haɗa da yi wa wasu mutane mugun nufi, ko sanya musu rashin jin daɗi saboda jinsinsu ko yin barkwanci kan jinsin mutum ko taɓa mutum ba da izininsa ba ko kuma yaɗa jita-jita ta jima’i.

Ya kamata iyaye su gargaɗi ‘ya’yansu kan cin zalin wasu yara, idan kuwa ɗanka ake zalunta, ya kamata ka yi gaggawar magance matsalar a matsayinka na uba ko uwa.

Daga MAHDI MUHAMMAD MUSA. ƙaramin Edita a jaridar Blueprint Manhaja. 07066778190.

By ukarofi