
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta kama Dakta Mkor Aondona, wanda shi ne mai taimaka wa gwamnan akan bincike da shirye-shirye bisa zargin yin lalata da ƙarbar kuɗaɗe a hannun masu laifi da nufin ɓoye bidiyon munanan ayyukansu.
A ranar Juma’a aka kama shi a Makurɗi bayan ɗalibai mata da dama sun shigar da ƙorafe-ƙorafe akansa, wanda suka zarge shi da cin zarafinsu da barazana a yanar gizo da kuma sharri.
An zargi Dakta Aondona da ɗaukar mata masu jan hankali aiki a taruka inda ya ke amfani da damar hakan wajen neman su ba shi kansu.
Haka kuma, an zarge shi da yin bidiyo a yayin lalata ba tare da sanin wanda ake yi da su ba, wanda daga bisani ya ke amfani da su wajen yi musu barazanar fitarwa matuƙar ba su cigaba da ba shi haɗin kai ba.
Haka kuma, ya kan aika wasu daga cikin bidiyoyin tsaraici na ƴan matan a kafafen sadarwa.
Kakakin EFCC Dele Oyewale ya ce nan ba da jimawa ba za a maka wanda ake zargin a kotu.
Lamarin ya haifar da cecekuce inda al’umma suke kira da a gaggauta ɗaukar mataki tare da tabbatar da yin adalci.
