JAMB ta shirya jarrabawar gwaji ga ɗalibai 96,838

Spread the love

Hukumar JAMB ta sanar da cewa za a gudanar da jarrabawar gwaji ta UTME ga ɗalibai 96,838 a ranar Asabar, 28 ga Yuni, 2025. JAMB ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Dr. Fabian Benjamin, ya fitar, inda ya bayyana cewa ɗaliban da abin ya shafa za su iya fara bugo takardun shaidar jarabawarsu daga Litinin, 23 ga Yuni.

Hukumar ta bayyana cewa wasu cibiyoyin CBT guda 113 sun samu dakatarwa ko cirewa daga jerin cibiyoyin da ke gudanar da jarrabawa sakamakon kama su da laifuka daban daban, ciki har da na fasaha da na aikata magudi. JAMB ta ce waɗannan cibiyoyi sun aikata laifuka ne a lokacin gwajin jarrabawa da kuma lokacin da aka gudanar da jarrabawar ta gaske.

A cewar JAMB, waɗanda za su amfana da wannan jarabawar sun haɗa da ɗaliban da suka kasa shigar da bayanansu ta hanyar na’urorin tantance sawun yatsa, da waɗanda suka rasa jarrabawar baya saboda wasu dalilai. Hukumar ta kuma bayyana cewa za a gudanar da wannan jarabawa a cibiyoyi 183 a fadin ƙasa, yayin da wasu ɗalibai daga garuruwan da aka soke za a sake tura su zuwa wasu makusantan wuraren da za su iya rubuta jarabawar.

JAMB ta yaba wa hukumomin tsaro da suka taimaka wajen binciken masu aikata laifin maguɗin jarrabawa, ciki har da wasu jami’anta da malaman makarantu. Haka kuma, ta yi kira ga ɗalibai da su kasance a cibiyoyin jarabawa kafin ƙarfe 8:00 na safe, lokacin da za a fara jarabawar. JAMB ta ja kunnen waɗanda ke niyyar aikata laifi da cewa za a ci gaba da fuskantar su da doka, musamman waɗanda ke rubuta jarabawa maimakon wasu.

By ukarofi