
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai ta Ƙasa (MOPPAN) ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga jarumar fina-finan Kannywood, Nollywood da kuma Bollywood, wato Rahama Sadau bisa rasuwar mahaifinta.
A sanarwar da ta fitar ta hannun Kakakinta, Ibrahim Amarawa, MOPPAN ta ce tana taya jarumar da ɗaukacin iyalanta da makusantanta jimamin babban rashin da aka yi musu.
Ta kuma ce, mahaifin nata ya yi rayuwa mai cike da ababen koyi ga ƴan baya duba da yadda ya kasance mai hikima kuma mai kirki wajen mu’amala.
MOPPAN ta yi fatan Allah ya ba su haƙurin juriyan rashin mamacin, wanda rayuwarsa ta yi kyakkyawar tasiri ga iyalansa da sauran al’umma.
Kazalika, ƙungiyar ta yi masa addu’ar samun rahama, inda ta ce Allah ya jiƙan sa ya kuma gafarta masa.
