Tinubu ya nemi a kafa jami’an ko-ta-kwana na ECOWAS yayin miƙa jagoranci ga Bio na Sierra Leone

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya miƙa ragamar jagorancin ECOWAS ga Shugaba Julius Maada Bio na ƙasar Sierra Leone, bayan kammala shekaru biyunsa a yayin taron ƙungiyar karo na 67, ranar Lahadi.

Gabannin haka ne aka samu raɗe-raɗen cewa akwai yiwuwar Bassirou Faye na Senegal ya gaje shi a kujerar.

A watan Yulin 2023 aka zaɓi Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS, inda kuma aka sake zaɓar sa shekara guda bayan haka a Abuja.

Tinubu ya samu ƙalubalen dawo da martabar dimukraɗiyya a shiyyar Afirka ta Yamma a lokacin da ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso suka fice daga cikin ƙungiyar bayan juyin mulkinsu.

A yayin jawabinsa na ƙarshe a matsayinsa na shugaba,Tinubu ya yi kira da a samar da jami’an tsaro na haɗaka na ko-ta-kwana don bunƙasa fannin a shiyyar.

Ya kuma nemi ƙasashen masu amfani da yaren faransanci da su dawo cikin ƙungiyar domin cigaba da tafiya tare da su don ciyar da shiyyar gaba.

By Babaji