
Sabon shugaban ECOWAS ya yi kira ga haɗin kai bayan kama aiki
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bio na Sierra Leone, wanda shi ne sabon shugaban Kungiyar ƙasashe masu Tattalin Arziƙi na Yammacin Afirka (ECOWAS) ya nemi ƙasashen da ke ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar da su haɗe kawunansu domin cimma nasarori a fannonin da suka saka a gaba.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi ragamar jagorancin ƙungiyar a ranar Lahadi a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja, bayan wa’adin Shugaban Bola Tinubu na biyu ya ƙare.
Ya ce, zai mayar da hankali kan ƙalubale da damanmaki da suke da su a shiyyar Afirka ta Yamma da ƙoƙarin fuskantar su bisa tsarin da ya dace.

Shugaba Bio ya kuma ce, sai an samu haɗin-gwiwa a tsakanin ƙasashe a fannin ci-gaban harkar tsaro wajen tunkarar sababbin ƙalubalen da ake fuskanta.
Sabon shugaban na ECOWAS ya ce shirin faɗaɗa harkar kasuwanci na ƙungiyar da kasuwanci a tsakanin iyakoki, za su taimaka wajen samar da ayyuka ga mata da matasa.
Daga bisani, ya yaba wa Shugaba Tinubu kan ƙoƙarinsa na samar da tsarin tattaunawa ta shiyya, farfaɗo da harkar tattali da gina zaman lafiya.
