Daga USMAN KAROFI
Adadin waɗanda suka rasa rayukansu a harin da aka kai wa matafiya a Mangu, Jihar Filato, yayin da suke hanyarsu ta zuwa bikin aure, ya ƙaru zuwa 12 bayan an gano ƙarin gawawwaki guda huɗu da aka binne a rami.
Shugaban sashen Jama’atu Nasril Islam (JNI) na ƙaramar hukumar Mangu, Alhaji Hudu Ibrahim Manomi, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa ranar Lahadi.
A cewar JNI, mutanen da suka mutu sun fito ne daga Basawa a Zariya, Jihar Kaduna, inda suke kan hanyarsu zuwa garin Kwa a ƙaramar hukumar Quan’pan, Jihar Filato, domin halartar bikin aure. Sai dai a Mangu aka tare su inda aka kai musu hari.
Rahotanni sun ce mutane takwas aka kashe tun farko, kuma an riga an binne su, yayin da aka ce huɗu sun ɓata. Bayan an kama wasu daga cikin waɗanda ake zargi, sai suka bayyana inda suka binne gawawwakin da suka ƙone kuma suka binne a rami kusa da fadar wani sarki a yankin.
JNI ta yi Allah-wadai da harin, tana mai cewa wannan kisan gilla na nuna rashin imani da ɗabi’a, kuma ya faru ne da rana tsaka.
Ƙungiyar ta miƙa ta’aziyyarta ga gwamnatin Kaduna, masarautar Zazzau, iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma al’ummar musulmi gaba ɗaya, tana roƙon Allah ya jiƙan mamatan.
Hakazalika, JNI ta buƙaci matasa da su guji ɗaukar doka a hannunsu, ta kuma nemi hukumomin tsaro su gaggauta gurfanar da waɗanda suka aikata wannan ta’asa domin a kafa misali ga sauran.
Shugabar mata ta JNI a Mangu, Habiba Shuaibu Aliyu, ta bayyana cewa bayan an kama wasu daga cikin waɗanda ake zargi, sun bayyana wurin da aka binne waɗanda suka kashe, lamarin da ya ƙara jefa jama’a cikin alhini da fargaba.
