Neja: Sojoji 17 da ƴan bindiga da dama sun rasu yayin karanbatta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kimanin jami’an sojoji guda 17 ne suka rasu a yayin musayar wuta tsakaninsu da ƴan bindiga a ƙauyen Bangi dake Ƙaramar Hukumar Mariga ta Jihar Neja.

A daren ranar Talata da misalin ƙarfe 11 na dare ne lamarin ya auku a lokacin da sojojin suka samu bayanai na sirri game da shigo wa Bangi da ƴan bindigar ke ƙoƙarin yi.

Yankin waje ne da ya shahara da aikata manyan laifuka da suka haɗa da garkuwa da mutane da satar dabbobi.

Muryoyi daga ƙauyen sun shaida wa manema labarai cewa a yayin da ƴan bindiga suke ƙoƙarin shiga garin ne sai sojojin suka yi musu kwanton-ɓauna inda aka ɗauki sa’o’i ana ba-ta-kashi a tsakaninsu.

A lokacin da ya ke jawabi game da lamarin, Shugaban Ƙaramar Hukumar, Abbas Kasuwa Garba ya ce harin ya faru ne a wurare biyu-Konan Dutse Kaiyan Ghana dake kusa da Bangi da kuma Gulunbi Boka da misalin ƙarfe 5 na yamma.

Ya kuma ce, a yayin bincike an samu gawawwakin sojoji guda 17 a dajin, waɗanda aka garzaya da su zuwa Barikin Sojoji dake Kontagora.

Ciyaman ɗin ya ƙara da cewa, ƴan bijilante da jami’an hukumomin tsaro suna gudanar da bincike a yankin dajin da abin ya faru, sannan da dama daga cikin ƴan bindigar sun rasa rayukansu.

Haka kuma, ya yaba wa rundunar sojojin sama bisa hoɓɓasa da suka yi wajen kai ɗauki a lokacin da ake fafatawa tsakanin ɓangarorin biyu, yana mai kira ga mazauna da su kwantar da hankali tare da ruwaito dukkan wani abin zargi ga hukumomin tsaro.

By Babaji