Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Taurari na ke nufi amma ba irin waɗanda Allah maɗaukakin Sarki ya dasa don jifar shaidanu ba don waɗannan na Haifa a arewacin Isra’ila daga hasken tartsatsin fadowar boma-bomai ne daga makamai masu linzami da Iran ke harbowa don maida martini ga harin da Isra’ila ta yi saraf ba ankararwa ta kai kan Iran don nuna ita ma aƙalla ta zama ‘yar sandar yankin gabar ta tsakiya. Na sha ba da labaru kan yanda Isra’ila kan kai hari lokacin da tag a dama cikin ƙasar Sham, Lebanon da Yaman ballantana ma yankin Gaza da ta mayar tamkar dandalin gwajin makaman kisan ƙare dangi ga mata da ƙananan yara. Gabanin ɗaukar mataki kan wata ƙasa akwai buƙatar bi ta hannun Majalisar ɗinkin Duniya da ɗaukar matsaya a kwamitin sulhu. A nan a na tsakiyar tattaunawa da Iran kan dakatar da shirin ta na haɗa makaman nukiliya sai kwatsam Iran ta kai ma ta farmaki. Na tabbata hukumar kula da makaman IAEA ba ta da hurumin turawa kai tsaye a aukawa wata kasa a irin wannan yanayi na neman samar da yarjejeniya. Kazalika ba Iran ce mai mallakar irin waɗannan makaman ba, ita Isra’ila da ke kai harin ta na da makaman kuma ba mu ga IAEA ta na matsa ma ta lamba ta wargaza masa’antun makaman ba. Hakan na nuna duniya a na rayuwar ‘yan bora da ‘yan mowa ne. Kwatsam yadda a ka wayi gari a babban birnin Iran wato Tehran da miyagun hare-hare daga Isra’ila:
Hari kan Iran: Tehran ta maida martani da gomman makamai kan Isra’ila:
Biyo bayan harin da Isra’ila ta kai kan Iran da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 78 ciki da manyan jagororin soja da sassan ƙera nukilya da makamai masu linzami, Iran ta maida martini da gomman makamai masu linzami kan Isra’ila.
Harin na Iran ya shafi birnin Kudus da Tel’aviv inda a ka ga hasken wutar makamai na karaɗe sararin biranen inda hukumomin Isra’ila su ka umurci mutane su shige maɓoyar kariya daga bom.
Tun farko Isra’ila kusan ta yi gaban kan ta wajen kai hari kan Iran yayin da a ke tattaunawa da Iran din kan neman dakatar da aikin ƙera makaman ƙare dangi.
Wannan shi ne za a iya cewa karo na farko da Iran ta auka cikin mummunan hari irin wannan tun fafatawa da Iraki a shekarun 1980.
Ba dai kamar yadda wasu ke hasashe wannan zai iya jawo yaƙin duniya na uku ba, in an duba yanayin martanin Iran kan ƙare ne ga ba da shaidar ta taɓuka wani abu amma ba ta ɗaukar matakin yaƙi na ‘yar gaba daya don hakan na da hatsari ga makomar ƙasar daga yanayin kurɗa-kurɗar siyasar duniya.
Shugaban addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei ya fusata ainun da wannan harin da ya kashe manyan jami’an tsaro a ƙasar don haka ya ce Iran za ta horar da Isra’ila.
Duk da yanzu wannan shi ne labari mai ci a duniya, amma ba zai yi wani dogon zango ba don za a iya sulhuntawa ko shashantar da maganar.
Saudiyya na kan gaba a ƙasashen Larabawa wajen yin Allah-wadai da wannan harin na Isra’ila.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce an dakatar da tattaunawa kan batun kafa ƙasar Falsaɗinawa gefe da ta Isra’ila biyo bayan harin da Isra’ila ta kai kan Iran.
Faransa da Saudiyya sun tsara za a gudanar da taro don tattaunawa kan samar da ƙasar Falasɗinu a gefe da Isra’ila gabanin harin da Isra’ila ta kai kan sassan masana’antun makamai Iran na ƙarƙashin ƙasa.
Kai tsaye an dage tattaunawar don ƙasashen yankin ba za su iya halartar taron daidai wannan lokaci na hari kan Iran.
Duk da haka Macron ya ce ya na goyon bayan kafa ƙasar Falsɗinawa da hakan shi ne matsayar Larabawa da za ta kawo maslaha a fitinar Isra’ila kan yankunan Falasɗinawa.
Tun ƙaddamar da hare-hare da Isra’ila ta yi kan jamhuriyar Musulunci ta Iran, an samu bayanai daga ɓangaren Iran ɗin masu bayyana cewa mutum 224 su ka rasa ran su.
Haka nan ita ma a martanin da Iran ta maida kan Isra’ila, hukumomin gwamnatin Yahudawa na bayyana cewa sun rasa mutum 24.
Shugaban addinin ƙasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya baiyana rashin girgizar Iran kan hare-hare da nuna lallai Isra’ila za ta girbi abun da ta shuka.
Shi kuma Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na cewa kasar sa na kan hanyar cimma burin farmaki kan Iran ta hanyar dakatar da Iran daga cigaba da ƙera makaman ƙare dangi da kuma daƙile ƙarfin tan a kai harin makami mai linzami.
Yanzu dai abun da ya fito fili a na cigaba da musayar wuta tsakanin ƙasashen biyu da dama ke zaman doya da manja da juna.
Koma dai me za a ce Amurka na matukar mara baya ga Isra’ila yayin da Iran ke aiki ita kaɗai in ka deɓe nuna abun da Isra’ila ta yi bai dace ba.
Aƙalla dai a na ganin ƙasar Rasha da Sin na marawa Iran baya ta bayan fage amma ba kamar yanda Amurka ke fitowa ƙarara ta na mara baya ga Isra’ila ba.
Abun fata a nan in ya zama an yi kare jinni biri jinni ya na da kyau a dakatar da hare-haren hakanan don kar a cigaba da asarar rayuka da yiwuwar neman ruguza ɗaukar Iran ta gwagwarmayar marigayi Ayatollahi Khumaini da ta fara jagorantar kasar a 1979.
Abun takaicin shi ne Isra’ila ba ta tantance inda za ta kai hari don a na tsakiyar aiki a gidan talabijin mallakar gwamnatin Iran sai Isra’ila ta kai wa gidan farmaki. Wato hakan ya nuna masu aikin yaɗa labaru ma ba su tsira ba. Wannan bai ban mamaki ba don rahoton yanda sojojin Isra’ila su ka harbe wakiliyar gidan talabijin na Aljazira Shireen Abu Akleh a yankin Jenin duk da yanda ta ke sanye da falmara mai rubutu gwara-gwara da ke nuna PRESS wato ‘yar jarida ce. Har yau ba wanda za a ce an hukunta kan wannan kisan gilla. Ba mamaki don ma ta na da tasiri da kuma samun dangi masu jajircewa kan neman haƙƙi ya sa a ka dan tattauna maganar kafin ta mutu murus.
Daidai lokacin da Isra’ila ke barin wuta kan Iran sai kawai shugaban Amurka Donald Trump ya fito ya na buƙatar Iran ta shiga sulhu kan makaman ƙare dangi. Duk mai hankali zai so ya ji Trump na neman a dakatar da hare-haren ne da farko kafin furta irin wannan matsaya. Ga dai wanda ya kai hari kuma a ka’idar shari’a wanda ya fara tada fitina shi ne azzalumi. Don haka yanzu dai an fahimci tamkar Amurka ta nada Isra’ila ta zama ‘yar sandar gabar ta tsakiya wajen ruwan wuta kan duk wanda ya daga ma ta yatsa. Cikin hakan ma sai a ka ji Trump na shawartar al’ummar da ke zaune a babban birnin Iran wato Tehran su fice daga birnin. A fili ya nuna wa imam Amurka za ta shigo yaƙin kai tsaye ko za ta cigaba da dumbulawa Isra’ila manyan makamai don daidaita Iran. Birnin Tehran fa babba ne kuma ya na ɗauke da fiye da mutum miliyan 9, ta yaya wani zai bushi iskar duniya ya umurci mutane da ke zaune a garin su cewa su fice daga garin? Shin in sun fice su kaura zuwa ina?
Gaskiyar Magana Iran ita kadai ba za ta iya kai wa har ƙarshen wannan yaƙi ita kaɗai ba don haka duk ƙawayen Iran musamman Sin da Rasha sai sun shigo don rage kaifin Amurka. Gaskiya ne Iran na ƙarfafa ƙungiyoyin da ke hamaiya da Isra’ila irin Hamas, Hezbollah da Houthi amma kai tsaye ai Iran bat a irin wannan yaki. Daga fara arangama da Isra’ila da Hamas ta yi daga ranar 7 ga Octobar 2023 shin manyan ‘yan Hezbollah da Hamas nawa ne Isra’ila ta kasha. Haƙiƙa Isra’ila ta yi kisa iya kisa kuma ko ramuwa ta ke yi haka ya wuce kowace irin gonad a iri. Haka fa Isra’ila ta sauke babban bom kan ofishin Hezbollah da ke Dahiyeh a kudancin Beirut inda hakan ya kashe shugaban Hezbollah din na tsawon lokaci Hassan Nasrallah da wasu abokan aikin sa. Za mu tuna wani cin zarafin Iran inda Isra’ila ta yi kisan gilla ga shugaban Hamas na tsawon lokaci Isma’il Haniyeh a birnin Tehran. Duk zaman da Haniyeh ya yi a birnin Doha na Katar bai sa Isra’ila ta kai ma sa mugun hari ba sai da ta bari ya shigo Tehran inda a ke tsammanin gagarumin tsaro. Gabanin nan ma mun tuna Isra’ila ta kai farmaki kan wani ofishin jakadanci na Iran da ke Damaskas ta kasha wasu kwamandojin Iran da a lokacin ke taimakawa tsohon shugaban Sham Bashar Al’asad.
KAMMALAWA
Sai ƙasashen gabar ta tsakiya sun tashi tsaye wajen kare ’yancin su, in ba haka ba za a wayi gari sun zama tamkar su na ƙarƙashin takubban Isra’ila ne kuma ba shugaban da zai daɗe kan karaga sai ya kai caffa birnin Tel’aviv. Ya zama wajibi ƙungiyar haɗin kan Larabawa ta yi taro don jan birki ta hanyar Allah-wadai da kyamatar hare-haren Isra’ila kan Iran duk da Iran ƙasar Farisawa ce. A nan ba ma maganar Sunnah da Shi’a na ke yi ba amma ina magana kan kare ’yanci ne da mutuncin ƙasashen na gabar ta tsakiya daga mulkin mallakar Isra’ila.
