Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
ƙungiyar ci gaban Gayawa da kewayenta ƙarƙashin shugabancin Bashir Ahmad Sani da ke ƙaramar hukumar Ungogo, ta yi taro don gabatar da kansu ga al’ummar Gayawa da kewaye da kuma gabatar da matsaloli biyar domin fuskantar matsaloli domin kawo ƙarshen su, wanda suka dakushe suka hana cigaba a wannan unguwa ta Gayawa, kamar dai yadda shugaban ƙungiyar Alhaji Bashir Ahmad Sani ya bayyana a lokacin taron wannan ƙungiya irinsa na farko tun bayan kafata a wata biyu da suka wuce.
Haka shugaban ƙungiyar cigaban Gayawa Malam Bashir ya ce matsalolin da suka addabe su su ne matsalar hanya, tsaro, lafiya, makaranta, da kuma maƙabarta wanda shi ne ya sa suka kira taro na kowa da kowa domin gabatar da kansu da kuma wannan matsaloli da kuma gudunmawar da kowa zai bayar domin warware wannan matsaloli daidai gwargwadon iyawarsa wani ta kuɗi wani ta shawara wani ta addu’a da dai sauran gudunmawa gwargwadon kishi da hali da mutum yake da shi a cewar shugaban.
Ya kammala da bayyana nasarori da ƙungiyar ta samu bayan kafata ta hanyar yin cikon ƙasa ga wata hanya da zaizayar ƙasa ta lalata ta wanda kimanin shekaru 35 hanyar bata biyuwa sai yanzu da suke wannan aikin sai kuma gina wata makaranta ta mata da sauran ayyuka na matsalolin da suka damu Gayawa inda ya ce sun kasha kuɗi sama da milliyan biyar ta hanyar yankawa junan su haraji da kuma faɗar mutum da kuɗin da ya bayar ta hanyar kafofin sadarwa na zamani inda kuma ya buƙaci kowanne mai gida ya tabbatar ya bada gudunmawarsa wajen tsaftar muhali ta hanyar yin kwalbati a duk gidan da aka gida da kwashe shara domin daƙile barazanar ambaliyar ruwa da zaizayar ƙasa, inda ya yaba wa gwamnati kan turo kwamishinan ayyuka ya ga matsalolinsu da kuma ɗaukan mataki wanda yanzu haka suna sauraron ganin ayyukan gwamnati ne a yanki da zaizayar ƙasa tayi katutu a unguwar Gayawa Kano Nijeriya.
